Hadimin gwamna Kashim ya kashe kansa a fadar gwamnatin Borno

Hadimin gwamna Kashim ya kashe kansa a fadar gwamnatin Borno

A yanzu din nan mun samu rahoton cewa, daya daga hadiman gwamnan jihar Borno Kashim Shettima, ya kashe kansa ta hanyar rataya a fadar gwamnatin dake birnin Maiduguri a Arewa maso Gabashin kasar nan.

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima
Source: Facebook

Kamar yadda Ndahi Inusa, majiyar mu ta reshen birnin Maiduguri ta bayyana, hadimin gwamnan, John Achagwa, ya rataye kansa jikin wani icen dogon yaro dake bayan farfajiyar saukar shugaban kasa a cikin fadar gwamnatin Borno da tsakar ranar Talata, 28 ga watan Mayu.

KARANTA KUMA: Rayuka 36 sun salwanta, an yi garkuwa da mutane 27 a fadin Najeriya a makon daya

Babu dalilin da ya sanya wannan hadimi ya yiwa kansa wannan mummunar aika-aika yayin da abokanan huldar sa suka bayar da shaidar su ta fahimtar yadda ya saba kasancewa kamar kullum yayin sauke nauyin da rataya a wuyan sa a bisa al'ada.

A yayin da wannan shi ne karo na farko da makamancin wannan lamari ya auku a fadar gwamnatin jihar Borno, gaggawar jami'an hukumar kwana-kwana wajen tunkarar lamarin ba tayi tasiri ba domin kuwa tuni hadimin ya ce ga garin ku nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel