Zaben jihar Kaduna: Tashin farko, El-Rufa'i ya doke Isa Ashiru a kotu

Zaben jihar Kaduna: Tashin farko, El-Rufa'i ya doke Isa Ashiru a kotu

Kotun zaben kujeran gwamnan jihar Kaduna a ranar Talata ta yi watsi da bukatar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na sake kirgan kuri'un da aka kada a zaben da ya gudana a watan maris, 2019.

Shugaban kotun, Alkali Ibrahim Bako, yayinda yake bada shari'ar ya ce kotun na da wa'adin kwanaki 180 kacal domin kammala sauraron karar saboda haka ba zata lamunci wani yunkurin sake kuirga kuri'u ba.

Bayan haka, kotun ta sake watsi da bukatar PDP bayan ta rage yawan kananan hukumomin da za'a sake kirga zuwa 12.

KU KARANTA: Kotu ta bada umurnin damke Akawun sarkin Kano, Danburam Kano da Mujitaba Abba

A ranar 25 ga watan Mayu, Lauyan PDP da dan takararta Isa Ashiru, Emmanuel Ukala, ya bukaci rage yawan kananan hukumomin zuwa 12 wadanda suka kunshi Kaduna ta arewa, Kaduna ta kudu, Igabi, Birnin Gwari, Giwa, Zaria, Sabon Gari, Makarfi, Kudan, Kubau, Soba da Ikara, inda jam'iyyar APC ta lashe zabe.

Ya dakatad da karar zuwa ranar 15 ga watan Yuni domin sauraron ainihin kara da PDP da ashiru suka shigar.

A bangare guda, Jam’iyyar Hope Democratic Party (HDP) ta daukaka kara a gaban kotun koli kan ta hana rantsar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 29 ga watan Mayu.

HDP ta daukaka karan ne inda ta nemi a soke hukuncin kotun sauraron karar zaben Shugaban kasa karkashin jagorancin Justis Joseph Ikyegh wanda a ranar 22 ga watan Mayu, ya ki amincewa da bukatar hana rantsar da Buhari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel