Magudin jarabawa: ICPC ta fara bincike kan jarabawar JAMB ta 2019

Magudin jarabawa: ICPC ta fara bincike kan jarabawar JAMB ta 2019

-Hukumar ICPC ta fara bincike domin bankado hakikanin gaskiyar lamarin da ya shafi magudin jarabawar JAMB ta 2019.

-A cewar hukumar ta ICPC duk wanda aka samu da hannu cikin laifin zai fuskanci hukuncin shari'a.

Hukumar yaki da rashawa da kuma ayyuka masu alaka da ita ICPC ta fara gudanar da bincike na musamman akan magudin jarabawar da aka samu yayin rubuta jarabawar JAMB din data gabata.

Daya daga cikin mambobin hukumar ce mai suna Mrs Olubukola Balogun ta sanar da hakan ga manema labarai a wata hira da tayi da su ranar Talata a Abuja.

Magudin jarabawa: ICPC ta fara bincike kan jarabawar JAMB ta 2019

Magudin jarabawa: ICPC ta fara bincike kan jarabawar JAMB ta 2019
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Zan zarce tare da wasu daga cikin ministocina, inji Buhari

Tace, hukamar na kan binciken magudin jarabawar wanda akwai sa hannun iyayen yara da kuma kungiyar wasu kwararrun masu rubuta jarabawar.

A cewarta hukumarsu na iya bakin kokarinta domin gano hakikanin gaskiyar lamarin. “ Muna da niyyar yin bincike tare da yin hukunci dangane da abinda bincikenmu ya bamu.

“ Muna kan yin aikin a yanzu haka domin samar wa hukumar JAMB da cikakken bayani akan magudin, ina da yakinin cewa zamuyi nasara a karshe.

“ Hukumar na kokarin sanin mene ne ya faru sannan kuma ta wace hanya za’a iya magance aukuwar hakan nan gaba,” a cewar ta.

Balogun tace duk wanda aka samu da laifi zasu gurfanar dashi a gaban shari’a. Ta bayyana magudin jarabawa a matsayin aiki na cin hanci, hukumar su tace sam baza ta bari irin wadannan miyagun ayyuka su cigaba da yaduwa a kasar nan ba.

Wata majiyar da ta fito daga kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN ta ruwaito cewa, shugaban hukumar JAMB farfesa Ishaq Oloyede ya bayyana cewa wasu iyayen na biyawa mutane 10 su rubutawa yaronsu daya jarabawar JAMB.

“ Zaka samu cewa irin wadannan yaran bayan sun je jami’a sai kaga hotonsa ya bambamta da hoton ainihin wanda ya rubuta jarabawar.” Inji farfesa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel