Da duminsa: Kotu ta bada umurnin damke Akawun sarkin Kano, Danburam Kano da Mujitaba Abba

Da duminsa: Kotu ta bada umurnin damke Akawun sarkin Kano, Danburam Kano da Mujitaba Abba

A yau Talata, 28 ga watan Mayu wata babban kotun majistare a jihar Kano ta bada umurin damke yan godan saurata uku, wanda ya hada da Mannir Sanusi, shugaban ma'aikatan fadar mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu.

Hukumar sauraron korafe-korafe da yaki da rashawa a jihar Kano ta shigar da karan wadannan mutane uku kotu ne kan rashin bayyana gaban hukumar domin amsa tambayoyi kan zargin badakalar bilyan hudu da ake yiwa sarkin Kano.

Alkalin majistaren, Muhammad Idris, ya bada umurnin damke Mannir Sanusi wanda ke rike da matsayin Danburam Kano; akawun sarkin Kano, Sani Muhammadu Kwari da Mujitaba Abba.

Da duminsa: Kotu ta bada umurnin damke Akawun sarkin Kano, Danburam Kano da Mujitaba Abba

Da duminsa: Kotu ta bada umurnin damke Akawun sarkin Kano, Danburam Kano da Mujitaba Abba
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Rayuka 36 sun salwanta, an yi garkuwa da mutane 27 a fadin Najeriya a makon daya

A baya mun kawo muku rahoton cewa Hukumar amsa korafe-korafe da yaki da rashawan jihar Kano tana shirin garkame shugaban ma'aikatan sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, Alhaji Munir Sanusi, kan rashin gurfana gaban hukumar domin amsa tambayoyi.

Kana za'a damke wasu ma'aikatan masarautar Kano biyu, Mujitaba Abba Sani da Sani Muhammad Kwaru, wadandan sukayi kunnen kashi kan gayyatar da hukumar domin amsa tambayoyi kan zargin da ake yiwa sarkin Kano na badakalar N4bn.

A labari mai kama da haka, Gammayar kungiyar yan Arewa masu rajin samar da cigaba da dimukradiyya, NADP ta soki lamirin mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II, inda ta nemi yayi gaggawar yin murabus daga sarautar Kano don kare mutuncin masarautar.

Kungiyar ta bayyana haka ne a ranar Alhamis, 23 ga watan Mayu a karshen taronta daga gudanar a babban birnin tarayya Abuja, taron daya samu halartar wakilanta daga jahohi 18 a Arewacin Najeriya inda suka tattauna batun matsalar tsaro a Arewa da kuma rikicin masarautar Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel