Sa'a 24 kafin rantsuwa, shugaban kasa Buhari ya gana da shugabannin tsaro na kasa a fadar Villa

Sa'a 24 kafin rantsuwa, shugaban kasa Buhari ya gana da shugabannin tsaro na kasa a fadar Villa

Yayin da bai wuce sa'a ashirin da hudu a rantsar da shi ba, shugaban kasa Muhammadu Buhari a halin yanzu ya shiga ganawar sirrance da shugabannin hukumomin tsaro na kasa cikin fadar sa ta Villa dake garin Abuja.

Ganawa tsakanin jagoran Najeriya da shugabannin hukumomin tsaro na kasa ta fara gudana ne da misalin karfe 2.00 na ranar Talata cikin ofishin shugaban kasa dake fadar sa Villa a babban birnin kasar nan na tarayya.

Babu masaniyar abin da ganawar za ta kunsa, sai dai an yi hasashen cewa tana da nasaba da shirin rantsar da Buhari a wa'adin gwamnatin sa na biyu da za a gudanar a harabar taro ta kasa Eagle Square dake garin Abuja a gobe Laraba, 29 ga watan Mayun 2019.

Kazalika an yi hasashen cewa ganawar na gudana ne biyo bayan ganawar shugaban kasa Buhari da kuma gwamnonin Arewa da ta wakana a ranar Litinin, inda suka kai masa koken kalubale na rashin tsaro da jihohin su ke fuskanta.

Sa'a 24 kafin rantsuwa, shugaban kasa Buhari na ganawa da shugabannin tsaro na kasa a fadar Villa

Sa'a 24 kafin rantsuwa, shugaban kasa Buhari na ganawa da shugabannin tsaro na kasa a fadar Villa
Source: Twitter

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel