Anyi garkuwa da mutane 2 yayinda yan bindiga suka kai hari kauyen Dan Ali

Anyi garkuwa da mutane 2 yayinda yan bindiga suka kai hari kauyen Dan Ali

Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu matasa biyu a kauyen Katsina. Daga cikin matasan da akayi garkuwa da su akwai Anas Idris wanda ya kasance dalibin jami’ar Umaru Musa Yar’adua, da kuma wani Ibrahim Jamilu.

Dukkanin matasan biyu jikoki ne ga wani dattijo mai suna Alhaji Sani Gambo, kuma anyi garkuwa da su ne a gidansu da ke kauyen Dan Ali na karamar hukumar Danmusa da ke jihar Katsina a jiya Litinin, 27 ga waan Mayu.

Yan bindigan wadanda suka kai farmak kauyen da misalin karfe 1:30 na tsakar dare, sun kuma sace wasu mata uku amma zuwa safiyar yau Talata, 28 ga watan Yuni suka sake su.

Anyi garkuwa da mutane 2 yayinda yan bindiga suka kai hari kauyen Dan Ali

Anyi garkuwa da mutane 2 yayinda yan bindiga suka kai hari kauyen Dan Ali
Source: Depositphotos

Wata majiya tace, an dawo da matan biyu cikin dare amm sai da safe suka samu damar zuwa gida.

“Jikokin mutumin na nan a hannusu, kuma har yanzu basu kira kowa ba” inji majiyar.

"Lokacin da suka iso garin, suna ta harbe-harben bindiga sannan suka shiga gidajen Alhaji Musa da na Sani Gambo. Ya tsufa sosai, kusan shekararsa 100. Yaran da aka sace sun kasance jikokinsa” cewar majiyar.

KU KARANTA KUMA: An samu nasarar kubutar da matar dan majalisa da 'ya'yansa guda biyu da aka sace a jihar Gombe

Har yanzu yan sanda ba su yi martani ka lamarin ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel