Basaja da aikin kwastam: An yanke wa wani mutum hukuncin daurin shekara 5

Basaja da aikin kwastam: An yanke wa wani mutum hukuncin daurin shekara 5

-Wani mutum mai basaja da aikin kwastam ya shiga hannun hukuma, inda aka yanke masa hukuncin daurin shekara 5 a gidan kaso.

-Mutumin mai shekaru 40 ya shiga hannun hukuma ne bayan da wadanda ya damfara suka farga cewa damfararsu kawai yayi kana sukayi kararsa zuwa wurin yan sanda.

Kotun majistare dake Apapa a jihar Legas ta aika da wani mutum dan shekara 40 gidan yari saboda yayi basaja da aikin kwastam tare da damfarar mutane kudi N454,000.

Mutumin mai suna Morgan Mohammed, ya samu kansa a kotu da zargin laifuka uku, wadanda suka hada da basaja, sata da yin karya a bayyane.

KU KARANTA:Zan karfafi ‘yan sanda da ma’aikatar shari’a, inji Buhari

Shugaban kotun T.O Babalola shi ne ya yanke wannan hukuncin bayan da wanda ake tuhumar ya amshi laifinsa. Kotu ta yankewa Morgan hukuncin daurin shekara 5 a gidan yari tare da biyan kudaden da ya damfari jama’a.

Wanda ake tuhumar dai zai kasance ne a gidan yari tsawon shekara 5 tare da aiki maitukar wuya wanda zai yiwa al’umma saboda laifin basajan da ya aikata.

Wanda ya shigar da wannan kara, Sajan Friday Inedu, ya sahidawa kotu cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne tsakanin watannin Agusta da kuma Oktobar 2018 a shiyar Agip estate dake jihar Legas.

Yace wanda ake tuhumar dai yayi basaja a matsiyan jami’in kwastam inda har ya samu damar karbar kudi N114,000 a hannun wasu mutane uku da zummar cewa zai sama masu aikin yi.

Inedu ya kara da cewa, akwai wasu N340,000 wanda ya karba daga hannun Vivian Nweke da Thelma Raji akan zai kawo musu buhu 30 na shinkafa ga kowanensu.

Bugu da kari wanda ake tuhumar ya sace kayayyakin da kudinsu ya kai N113,000 daga wurin Raji. Wadanda aka karbi kudadensu ne suka kai karar wannan mutum wurin yan sanda bayan sun fahimci damfara ce kawai ya shirya masu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel