Buhari ba zai nuna wariya ba wajen kafa sabuwar Majalisar sa - Moghalu

Buhari ba zai nuna wariya ba wajen kafa sabuwar Majalisar sa - Moghalu

Cif George Moghalu, babban mai kula da harkokin shige da ficen kudi na jam'iyyar APC, yayi tsokaci kan wasu ababe da suka shafi gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin da ta ke gab ta shiga cikin wa'adin ta na biyu.

Babban jigon na jam'iyyar APC yayin hirar sa da manema labarai na jaridar Daily Trust a karshen makon da ya gabata, ya yi sharhi kan wasu muhimman ababe da suka shafi kasar nan da kuma yadda ake sa ran gwamnatin shugaban kasa Buhari za ta kasance a wa'adi na biyu.

Buhari tare da jiga-jigan jam'iyyar APC na kasa

Buhari tare da jiga-jigan jam'iyyar APC na kasa
Source: Facebook

Cif Moghalu ya ce sabanin nasarori da kuma kwazon shugaba Buhari a wa'adi na farko, gwamnatin sa ta fuskanci wasu manyan kalubale musamman a fannin tsaro da kuma tattalin arzikin kasa.

Ire-iren kalubale da gwamnatin Buhari ta fuskanta kamar yadda jigon na APC ya bayar da shaida na da babbar nasaba ta rikicin makiyaya da manoma, ta'addancin kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram, garkuwa da mutane da kuma faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya.

KARANTA KUMA: Bayan kwanaki 250, Buhari bai dauki hukunci kan Ministan sa da aka kama da laifi ba

Dangane da kafa sabuwar majalisar Buhari a wa'adi gwamnatin sa na biyu, Cif Moghalu cikin yakini da sa rai, ya ce ko kadan Buhari ba zai nuna wariya ga kowace jiha ko kuma wani yanki a kasar nan ba wajen samar da 'yan majalisar da za su taya sa riko na akalar jagoranci.

Yayin tsokaci akan katutu na talauci da mafi akasarin al'ummar kasar nan ke kuka da shi, babban jigon na APC ya ce shugaba Buhari na iyaka bakin kokarin sa wajen inganta jin dadin rayuwar al'umma duk da cewa ko a kasar Amurka ana fama da wani kaso na Yunwa da kuma Talauci.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel