Kotu ta daure wanda ya fallasa zargin gwamnan CBN da satar biliyoyi

Kotu ta daure wanda ya fallasa zargin gwamnan CBN da satar biliyoyi

Wani mutum da ya fallasa zargin gwamnan babban bankin kasa (CBN), Godwin Emefiele, da tafka almundahana ya samu matsuguni a gidan yari bayan ya bayyana cewar Emefiele bai cancanta ya zarce a matsayin gwamnan CBN na wani zangon ba.

Kotu ta bayar da umarnin a tsare mutumin, George Uboh, shugaban wata kungiya mai zaman kanta da ake kira 'Uboh Whistleblowers', a gidan yari na Suleja a ranar 23 ga watan Mayu bayan Emefiele ya shigar da karar zarginsa da bata masa suna.

Lauyansa, John Mary Jideobi, ya ce an kama Uboh a harabar kotu ne bayan an bayar da belinsa a kan wata shari'ar daban.

Uboh ne ya fara shigar da karar Emefiele a gaban wata kotun tarayya dake Abuja, yana mai kalubalantar yunkurin gwamnatin tarayya na sabunta nadin Emefiele a matsayin gwamnan CBN a karo na biyu.

Kotu ta daure wanda ya fallasa zargin gwamnan CBN da satar biliyoyi

Gwamnan CBN; Godwin Emefiele
Source: Depositphotos

A takardar karar mai lamba kamar haka: FHC/ABJ/CS/419/2019, Uboh ya nemi kotun ta dakatar da sake nadin Emefiele.

DUBA WANNAN: Sanatoci sun nuna kyashi a kan N160m da FIRS ta ware domin walwalar direbobi 850

Uboh na zargin Emefiele da hada kai da kamfanin dillancin man fetur na kasa (NNPC) wajen zambatar 'yan Najeriya kudaden da yawansu ya kai biliyan N500.

Duk da kotu ta nemi Emefiele ya bayyana domin kare kansa, bai yi hakan ba har majalisa ta tabbatar da shi.

Jami'an 'yan sanda na rundunar binciken miyagun laifuka (FCID) ne suka kama Uboh kafin daga bisani su gurfanar da shi a gaban kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel