Za a rantsar da zababben gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni cikin sirri

Za a rantsar da zababben gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni cikin sirri

Za a rantsar da zababben gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu a matsayin sabon gwamna a cikin sirri.

Jaridar the Nation ta ruwaito cewa halartan taron zai kasance akan gayyata , kamar yadda aka buga katin gayyata sannan aka bai wa manyan jami’ai kadai a matsayin tikitin da zai ba mutum dammar shiga dakin taron.

Shugaban labaran kwamitin rantsar da gwamnan na 2019, Alhaji Mala Musti wanda ya kuma kasance kwamisinan labarai na jihar, ya bayyana wa manema labarai a Damaturu cewa za a gudanar da taron ne a dakin taro na gidan wamnati da ke Damaturu sannan kuma za a tsaurara kula da cunkoso a dakin taron.

Za a rantsar da zababben gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni cikin sirri

Za a rantsar da zababben gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni cikin sirri
Source: Twitter

Kwamishinan ya shawarci jawa’a da ba za su samu damar halartan taron ba da su jira har zuwa ranar 12 ga watan Yuni lokacin da za a yi babban biki filin wasa na August 27 da ke Damaturu.

KU KARANTA KUMA: 29 ga Mayu: Kano ta kaddamar da yau Talata a matsayin ranar addu’a a fadin kananan hukumomi 44

Yayi bayanin cewa hukuncin kwamitin na rantsar da gwamnan cikin sirri ya kasance saboda bikin rantsar da Shugaban kasa da za a yi cikin sauki a Eagle Square Abuja.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel