Ya zama dole Buhari ya janye tallafin man fetur –Kwararre akan tattalin arziki

Ya zama dole Buhari ya janye tallafin man fetur –Kwararre akan tattalin arziki

-Wani masanin harkokin tattalin arziki yayi fashin baki akan kasafin kudin 2019 da kuma janye tallafin man fetur.

-Masanin yace gwamnati na damar janye tallafin idan dai har tana so ta aiwatar da kasafin N8.92trn kammar yadda aka tsara.

Hanya daya ce wacce Shugaba Muhammadu Buhari zai bi domin samun aiwatar da abinda ke kunshe cikin kasafin kudin shekarar 2019 tare da biyan mafi karancin albashin N30,000 ita ce janye tallafin man fetur, a cewar wani masani akan tattalin arziki, David Ibidapo.

Masanin yayi wannan bayanin ne jim kadan bayan shugaban ya sanyawa kasafin kudin 2019 hannu a ranar Litinin.

Ya zama dole Buhari ya janye tallafin man fetur –Kwararre akan tattalin arziki

Ya zama dole Buhari ya janye tallafin man fetur –Kwararre akan tattalin arziki
Source: UGC

KU KARANTA:Zan karfafi ‘yan sanda da ma’aikatar shari’a, inji Buhari

Da yake zantawa da kamfanin dillacin labarai na Najeriya NAN, yayi tsokaci akan karin N90bn da kasafin ya samu inda yake cewa shugaban nada babban kalubale a gabansa kafin ya samu damar aiwatar da kasafin kudin tare da biyan mafi karancin albashi.

Ya sake cewa, gwamnati zata kashe makudan kudade domin ta samu damar biyan mafi karancin albashi, a daidai lokacin da kasar ke bukatar samun kudaden shiga.

“ Hanya guda dayace zata baiwa gwamnati damar kaddamar da kasafin kamar yadda ta tsara, ita ce na toshe duk wata baraka da bai zama wajibi gwamnatin ta rika yi ba, ba lallai sai tallafin man fetur ba.

“ Amma idan har za’a janye tallafin man, ko shakka babu gwamnatin zata ji dadin hakan. Domin yin hakan sauki ne a gareta. Kari akan wannan, yakamata a ce gwamnati nada hanyoyi da dama na samarwa kanta kudaden shiga wanda zai kara habbaka tattalin arziki.” A cewar masanin.

Shugaba Buhari ya sanyawa kasafin kudin na N8.92tn hannu bayan majalisar dokokin tarayya ta kawo masa kasafin kamar yadda doka ta tanada. Abinda ya rage yanzu kawai aiwatar da abinda kasafin kudin ya kunsa ne.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel