Sanatoci sun nuna kyashi a kan N160m da FIRS ta ware domin walwalar direbobi 850

Sanatoci sun nuna kyashi a kan N160m da FIRS ta ware domin walwalar direbobi 850

- Kwamitin hadin gwuiwa majalisun Najeriya mai kula da al'amuran hukumar tattara haraji ta tarayya (FIRS) ya nuna damuwar sa a kan batun harajin biliyan N146.54 da hukumar ta ce zata samu daga bangarorin da basu da alaka da man fetur

- Shugaban FIRS, Tunde Fowler, ya bayyana cewar hukumar ta ware miliyan N160 domin dinka wa direbobin su 850 kayan aiki

- Kazalika ya bayyana cewar hukumar ta are miliyan N825 domin walwalar direbobi da kuma wata miliyan N250 domin tsaro

Kwamitin hadin gwuiwa majalisun Najeriya mai kula da al'amuran hukumar tattara haraji ta tarayya (FIRS) ya nuna damuwar sa a kan batun harajin biliyan N146.54 da hukumar ta ce zata samu daga bangarorin da basu da alaka da man fetur a cikin shekarar 2019.

Da suke nuna damuwar su a kan hakan, shugaban kwamitin, Sanata John Enoh, tare da ragowar mambobin kwamitin sun nemi karin bayani a kan yadda harajin na shekarar 2019 ya ragu da kaso 4.75% idan aka kwatanta da wanda FIRS tayi hasashen samu a cikin kasafin kudin shekarar 2018.

Sanatoci sun nuna kyashi a kan N160m da FIRS ta ware domin walwalar direbobi 850

Majalisar dattijai
Source: UGC

Kazalika kwamitin ya nuna wata damuwar a karin kudin jin dadin ma'aikatan FIRS da kaso 14% idan aka kwatanta da na shekarar 2018. Kwamitin ya nemi ba'asin yadda FIRS ta ce za tayi amfani da miliyan N160 domin dinka wa direbobin hukumar kayan aiki, miliyan N825 domin walwala da kuma wata miliyan N250 domin tsaro.

DUBA WANNAN: Muhimman abubuwa 10 da Buhari ya fada yayin hira da shi

Da yake kare kasafin kudin, shugaban hukumar FIRS, Tunde Fowler, ya ce karin kudin walwalar ma'aikata na da nasaba da karin ma'aikatan da hukumar zata dauka a cikin shekarar 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel