Wata sabuwa: Shuwagabannin APC sun bukaci Oshiomole yayi murabus

Wata sabuwa: Shuwagabannin APC sun bukaci Oshiomole yayi murabus

Wata sabuwar rikici ta kunno kai tsakar gidan jam’iyyar APC, inda wasu daga cikin jiga jigan jam’iyyar da shuwagabanninta suka nemi shugaban jam’iyyar tasu, Adams Oshiomole da yayi murabus, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yawancin shuwagabannin jam’iyya dake da wannan ra’ayi suna danganta hakan ne ga rashin tabuka wata katabus da Oshiomole yayi tun bayan darewarsa mukamin shugabancin jam’iyyar.

KU KARANTA: Ku cigaba da yi ma Sarki Sunusi biyayya – Masarautar Kano ga hakimai

Wata sabuwa: Shuwagabannin APC sun bukaci Oshiomole yayi murabus

Wata sabuwa: Shuwagabannin APC sun bukaci Oshiomole yayi murabus
Source: Twitter

Idan za’a tuna a yan kwanakin nan an samu hukunce hukuncen kotun mabanbanta da suka warware nasarorin da wasu yan takarkarun jam’iyyar APC suka samu a matakan siyasa daban daban, inda kotunan suka kwace kujerun jam’iyyar suna mika ma jam’iyyun adawa, musamman a jahar Zamfara.

Masana harkokin siyasa da dama sun bayyana wannan koma baya da jam’iyyar APC ta samu ga irin tsarin zaben fidda gwani da jam’iyyar a karkashin jagorancin Adams Oshiomole ta kirkiro ne, hakan tasa aka dinga tafka katobara a zabukan tare da gwara kan yan jam’iyya.

Ko a ranar Litinin data gabata sai da mataimakin shugaban jam’iyyar APC reshen Arewacin Najeriya, Sanata Lawan Shuaibu ya rubuta wata wasika ga shugaban jam’iyyar yana sukar yadda yake tafiyar da jam’iyyar, tare da nuna masa gazawarsa, da kuma rashin kwarewa a harkar siyasar jam’iyya.

Kunshe a cikin wasikar, Lawan yayi kira ga Oshiomole yayi murabus cikin ruwan sanyi tunda dai babu wani cigaba daya kawo ma APC, kuma yace da a kasashen waje inda aka cigaba ya aikata irin haka da da kansa zai yi murabus ba sai an tursasashi ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel