Bayan kwanaki 250, Buhari bai dauki hukunci kan Ministan sa da aka kama da laifi ba

Bayan kwanaki 250, Buhari bai dauki hukunci kan Ministan sa da aka kama da laifi ba

A yau ne ya cika daidai kwanaki dari biyu da hamsin bayan samun Ministan sadarwa, Adebayo Shittu, da laifin kaurace wa yiwa kasa hidima a hukumar nan ta bautar kasa NYSC. Masu sharhi sun ce Ministan ya aikata laifin ne da gangan.

Babu kuskure ko rafkanuwa, Ministan sadarwa Adebayo Shittu ya tsallake yiwa Najeriya bauta ta tsawon shekara daya kacal kamar yadda hukumar NYSC tayi tanadi. Hukuncin wannan laifi a dokar kasa sa bai wuce dauri na watanni 12 a gidan Dan Kande.

Sashe na 2 sakin layi na farko cikin kundin tsarin hukumar NYSC, ya tilasta yiwa Najeriya hidima ta tsawon shekara daya kacal a kan duk dan asalin kasar nan da ya kammala karatun digiri ko kuma karatun babbar Difloma a nan gida ko kuma a kasashen ketare.

Ministan sadarwa Adebayo Shittu

Ministan sadarwa Adebayo Shittu
Source: UGC

Kazalika an shar'antawa dukkanin masu daukar aiki a kasar nan da su bukaci takardar shaidar yiwa Najeriya hidima ga mabukata da manema aiki a matsayin wani bigire na sharadin daukan aiki a kasar nan.

Wannan hukunci ya fi karfi da kuma tasirin gaske musamman akan ma'aikatan gwamnati da za su yiwa al'umma hidima a ma'aikaru da cibiyoyin gwamnati daban daban.

Shakka ba bu doka ta ba damar kaurace wa yiwa Najeriya hidima ga wadanda shekarun haihuwar su suka haura talatin yayin kammala karatuttukan su. Akwai kuma wadanda kasa ta karrama da kuma masu yiwa kasa hidima a hukumomin dakarun tsaro na soji da 'yan leken asiri.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, bayan Ministan sadarwa Adebayo Shittu da aka kama da wannan mummunan laifi, akwai kuma tsohuwar Ministar kudi a gwamnatin Buhari, Kemi Adeosun, da aka kama tana amfani da takardun shaidar yiwa kasa hidima na bogi.

KARANTA KUMA: Talakawan Najeriya ne kadai ke son gani na a kujerar mulki - Buhari

Bayan fuskantar matsin lamba da tayi, tun a watan Satumba na shekarar 2018 da ta gabata tsohuwar Ministan ta yi murabus tare da arcewa daga kasar Najeriya cikin hanzari ba tare da fuskantar wani hukunci na laifin da ta aikata ba.

A sanadiyar wannan takaddama ta kauracewa yiwa kasa hidima, ya sanya jam'iyya mai ci ta APC ta yi fatali da kudirin ministan sadarwa Adebayo Shittu, yayin zaben fidda gwanin takarar kujerar gwamnan jihar Oyo.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel