Kasafin kudi: Ka kuka da kanka amma ba da majalisar dokoki ba – Dogara ga Buhari

Kasafin kudi: Ka kuka da kanka amma ba da majalisar dokoki ba – Dogara ga Buhari

Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, a ranar Talata, 28 ga watan Mayu yace shugaban kasa Muhammadu Buhari kuka da kansa akan jinkiri da aka samu wajen amincewa da kasafin kudi na 2019 ba da majalisar dokokin kasa ba.

Buhari wanda a ranar Litinin, 27 ga watan Mayu ya sa hannu a kasafin kudin 2019, ya tabbatar da rashin amannansa akan Dogara da shugaban majalisan dattawa, Bukola Saraki.

Har ila yau, Dogara yace tun daga lokacin da shugaban kasa Buhari ya shiga ofis, bai taba iya gabatar da kasafin kudi ba a lokaci.

Kasafin kudi: Ka kuka da kanka amma ba da majalisar dokoki ba – Dogara ga Buhari

Kasafin kudi: Ka kuka da kanka amma ba da majalisar dokoki ba – Dogara ga Buhari
Source: UGC

A wani jawabin da Ya sa hannu, Dogara yace: “Kasafin kudin shi na farko ya kasance na 2016 wanda ya gabatar a ranar 22 ga watan Disamba, 2015, kimanin kwana tara kafin karewar kasafin kudin shekarar.

“Karancin lokacin da majalisar dokoki ke bukata don amincewa da kasafin kudi watanni uku ne.

KU KARANTA KUMA: Na raina irin kishin-kasar Saraki da Dogara a Majalisa inji Shugaba Buhari

“Amman ya gabatar da shi kwana tara kafin shiga 2016 sannan abunda yan Najeriya basu sani ba kuma shugaban kasar ba zai fada ba shine majalisar zartarwa da hadin kan ma’aikatu sun cigaba da bada shawaran kara tulin ayyuka a kasafin kudin 2018 har zuwa watan Afrilu da Mayu wanda hakan yayi sanadiyar jinkirta amincewar kasafin kudin 2018.

“An bada sanarwan ne ga hukumomi kuma idan kuna shakka, akwai wasiku da kwanan watansu wadanda aka rubuto aka kuma karba. Amman ga Buhari yana daura ma majalisan dokoki alhaki.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel