Talakawan Najeriya ne kadai ke son gani na a kujerar mulki - Buhari

Talakawan Najeriya ne kadai ke son gani na a kujerar mulki - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin da ta gabata ya bayyana cewa tun fil azal manyan 'yan Najeriya ba su taba goyon bayan kudirin sa na siyasa wajen kasancewar sa jagora a kasar nan.

Sai dai shugaban kasar ya ce a halin yanzu ya zama tilas manyan kasa su yi godiya ga talakawan Najeriya da suka yi tsayuwar daka tare da jajircewa wajen tabbatar da kasancewar sa shugaban kasa da zai tsamo kasar nan daga kangi na gazawa ta fuskar jagoranci.

Talakawan Najeriya ne kadai ke son gani na a kujerar mulki - Buhari

Talakawan Najeriya ne kadai ke son gani na a kujerar mulki - Buhari
Source: Twitter

A cewar Buhari manyan Najeriya ba za su gushe ba wajen ganin bayan duk wani mai neman kujerar mulki da ke da manufa da ta sabawa burace-buracen zuciyar su a fannin siyasa da kuma tattalin arziki.

Lafazin shugaban kasa Buhari na zuwa ne yayin wata hira da ya gudanar a kafar watsa labarai ta kasa NTA a daren Litinin. Ya ce tarin dukiya ta manyan Najeriya ba ta yi tasiri ba wajen hana talakawan kasar nan tabbatar da kasancewar sa jagora.

KARANTA KUMA: 2023: Ko a siyasar ma ba kada wani galihu - Peter Obi ya yi kaca-kaca da Amaechi

Buhari ya ce domin neman samun shiga a wurin talakan kasar nan ba bu wata karamar hukuma a Najeriya da bai ratsa cikin ta ba a tsakanin shekarar 2003 kawo wa yanzu a yayin shawagin sa na yakin neman zabe.

Hirar shugaban kasa Buhari na zuwa ne yayin da ya rage saura kwanaki biyu kacal a rantsar da shi a wa'adin gwamnatin sa karo na biyu. Ko shakka babu Buhari ya lashe babban zaben kasa da kimanin kuri'u miliyan hudu yayin zaben da aka gudanar a watan Fabrairun da ya gabata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel