29 ga Mayu: Kano ta kaddamar da yau Talata a matsayin ranar addu’a a fadin kananan hukumomi 44

29 ga Mayu: Kano ta kaddamar da yau Talata a matsayin ranar addu’a a fadin kananan hukumomi 44

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana ranar Talata, 28 ga watan Mayu a matsayin ranar addu’a a fadin kananan hukumomi 44 duk daga cikin bikin ranar rantsarwa wacce tayi daidai da Laraba, 29 ga watan Mayu.

Shugaban kwamitin rantsarwa mai dauke da mutane 100 kuma Sakataren gwamnatinjihar, Alhaji Usman Alhaji, ya bayyana haka ga manema labarai a Kano a ranar Litinin, 27 ga watan Mayu.

Ya fbayyana cewa ko da yake bikin wannan shekarar ba zai kasance da shagali ba kamar yanda aka saba, za a gudanar da ayyuka da dama wanda daga ciki akwai addu’o’i da za a gabatar don zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin kananan hukumomi 44.

29 ga Mayu: Kano ta kaddamar da yau Talata a matsayin ranar addu’a a fadin kananan hukumomi 44

29 ga Mayu: Kano ta kaddamar da yau Talata a matsayin ranar addu’a a fadin kananan hukumomi 44
Source: Twitter

Ya kara bayyanawa cewa mai girma gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje zai gabatar da jawabi duk cikin shirye-shiryen inda gwamna zai bayyana shirin da gwamnatinsa ta tanadar wa al’umman jihar, cikin shekaru hudu masu zuwa.

KU KARANTA KUMA: Gidan aro: Almakura ya mika wa Sule makullen gidan gwamnatin Nasarawa

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Hukumar amsa korafe-korafe da yaki da rashawan jihar Kano tana shirin garkame shugaban ma'aikatan sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, Alhaji Munir Sanusi, kan rashin gurfana gaban hukumar domin amsa tambayoyi.

Kana za'a damke wasu ma'aikatan masarautar Kano biyu, Mujitaba Abba Sani da Sani Muhammad Kwaru, wadandan sukayi kunnen kashi kan gayyatar da hukumar domin amsa tambayoyi kan zargin da ake yiwa sarkin Kano na badakalar N4bn.

Hukumar ta shirya tsaf domin shigar da kara kotun Majistare a yau domin samun ikon damkesu, wani majiya a hukumar ya laburta.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel