Tirkashi: Donald Trump ya ce 'yan Afirka ba mutane ba ne

Tirkashi: Donald Trump ya ce 'yan Afirka ba mutane ba ne

- Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce bai kamata a dinga kiran 'yan Afirka da mutane ba

- Ya ce muddin ace kuna da zinare, lu'u-lu'u, man fetur, karafa da wasu abubuwan arzikin kasa amma ace al'ummar ku na zaune cikin wahala da yunwa, bai kamata a kira wadannan al'umma da mutane ba

A wannan karon ma shugaaban kasar Amurka, Donald Trump ya sake wata magana mai harshen damo akan al'ummar nahiyar Afirka, a wannan karon shugaban yana tambayane, anya mutanen nahiyar Afirka sun cancanci a dinga kiransu da mutane kuwa?

Ya ce, "Idan har kuna da zinare, lu'u-lu'u, man fetur, karfe da sauransu, kuma amma ace al'ummar yankin na cikin wahala da yunwa, ban tunanin wadannan mutanen sun cancanci a kira su mutane."

Ga wasu manyan tambayoyi guda biyar da shugaban kasar yayi wa shugabannin kasashen Afirka.

"Ba na bukatar na razanaku kamar yadda shugaban kasar Faransa yayi, inda yace karshen Afirka ya zo, amma duk da haka sun cigaba da turo muku 'yan leken asiri a matsayin masu zuwa yawon bude ido suna daukar sirrinku suna kai musu."

"Idan har baya da shekaru 50 da samun 'yancin kai baku gina ababen more rayuwa ga al'ummarku ba, ban tunanin ku mutanene? "

KU KARANTA: Babu adalci a hukunci da kotu ta yanke a jihar Zamfara - Adams Oshiomhole

"Idan har kuna da zinare, lu'u-lu'u, man fetur, karfe da sauransu, kuma amma ace al'ummar yankin na cikin wahala da yunwa, ban tunanin wadannan mutanen sun cancanci a kira su mutane?"

"Idan har kuna mulkar kasashen ku, sannan kuma kuna zuwa gurin wasu kasashe sayen makamai domin yakar mutanen ku, mutane baza su yi haka ba?"

"Idan har burin ku na rayuwa shine kawai ku dauwama akan mulki, mutum baya wannan tunanin?"

"Idan har kun mayar da rayukan mutanen ku tamkar na kiyashi, wanene zai ga darajarsu?"

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel