Wasu Gwamnoni su na gaggauta bada kwangiloli a karshen wa’adin su

Wasu Gwamnoni su na gaggauta bada kwangiloli a karshen wa’adin su

Kwangilolin karshe da gwamnonin jihohi masu barin gado su ke badawa a halin yanzu zai jawo rikici tsakanin su da Magadansu. Jaridar Daily Trust ta kasar nan tayi wannan dogon bincike a makon nan.

Wasu wamnonin da su ka sha kasa a zaben bana, ko kuma wa’adinsu ya kare su na raba wasu kwangiloli barkatai a karshen wa’adinsu. Wannan ya jawo surutu daga cikin gwamnonin da za su karbi mulki.

A irin su jihar Adamawa inda Ahmadu Umaru Fintiri zai canji gwamna Jibrilla Bindow, an fara samun wannan matsala inda har sabon gwamnan ya sha alwashin binciken gwamnatin APC a jihar ta Adamawa.

Bindow ya raba wasu filaye da za a gina shaguna a kan katangar nakarantar mata da ke Yola da kuma wata babbar kasuwa da ke Garin Jimeta. Fintiri ya rantse zai dakatar da wannan aiki da zarar ya hau mulki.

A jihar Ogun, Amosun ya dauki mutane fiye da 1000 aiki yayin da yake shirin barin mulki. Haka zalika ya nada sababbin Sakatarorin din-din-din, tare da kafa majalisar da za ta rika lura da jami’ar MAUSTECH.

KU KARANTA: Gwamnan Ogun zai bar mulki da Allah-ya-isan Ma’aikata

A jihar Bauchi ma dai akwai irin wannan rikici inda gwamna Mohammed Abubakar ya bada kwangilar sayen wasu manyan motoci masu tsada. Gwamnan ya kuma yi yunkurin ba SUBEB wasu kwangiloli kwanaki.

Ibrahim Dankwambo ya tsiri raba wasu ayyuka a daidai lokacin da mulkinsa ya zo karshe. Bayan nan kuma jihar na fama da tarin jami’o’i cikin gida har biyu da kuma dinbin bashi da sabon gwamna zai gada.

A jihar Kwara gwamna Abdulfattah Ahmed ya na ta raba mukamai barkatai, amma wanda ya fi fitowa fili shi ne nada sabon shugaban jami’ar jihar da ke Malete yayin da wa’adin Farfesa Abdulrasheed Na’allah bai kare ba.

A Zamfara kuma, gwamna Abdulaziz Yari ya fara shirin yi wa masarautun jihar kwaskwarima. A irin su Oyo da Imo, ana fama da irin wadannan rikici inda gwamnonin ke gaggawan nada mukamai da fitar da wasu kudi.

A Yobe, Nasarawa da Legas da kuma jihar Borno, watakila ba za a samu sabani tsakanin gwamnonin da za su bar mulki da kuma Magadan na su ba, ganin cewa kusan ba a samu wata ta-ta-burza a yakin zabe ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel