Buhari ya yi alhinin mutuwar Dr Ibrahim Lame

Buhari ya yi alhinin mutuwar Dr Ibrahim Lame

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika sakon ta'aziyya ga iyalin Dr Ibrahim Yakubu Lame bisa rasuwar tsohon jigon na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) kuma tsohon Ministan harkokin 'Yan sanda.

Sakon ta'aziyyar shugaba Buhari na kunshe ne cikin wani jawabi da kakakinsa, Malam Garba Shehu ya fitar inda ya ce jigon na APC ya yiwa kasa hidima sosai har zuwa rasuwarsa.

Ya ce marigayin mutum ne mai "ilimi sosai da zurfin tunani".

Buhari ya yi alhinin mutuwar Dr Ibrahim Lame

Buhari ya yi alhinin mutuwar Dr Ibrahim Lame
Source: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sunyi garkuwa da mai shirya fina-finai, sun nemi N10m

"Ya yiwa jam'iyya da kasa hidima sosai. Shi da wasu tsirarun sunyi tafiye-tafiye zuwa jihohi daban-daban a Najeriya suna isar da sakon jam'iyyar APC a lokacin da aka kafa jam'iyyar wanda hakan ya yi tasiri wurin nasarar da jam'iyyar ta samu a 2015 da Fabrairun wannan shekarar," a cewar shugaban kasar.

A karshe, Buhari ya yi addu'ar Allah ya ji kansa, ya sa aiyukansa na alheri su zame mata garkuwa, ya kuma bawa 'yan uwa da abokansa na arziki da gwamnati da al'ummar jihar Bauchi hakurin jure rashin sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel