Gwamna Masari ya nemi a daina biyan masu garkuwa kudin fansa

Gwamna Masari ya nemi a daina biyan masu garkuwa kudin fansa

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, ya bukaci al’umma da su dakatar da biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a fadar Shugaban kasa bayan ganawar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi da gwamnonin arewa a ranar Litinin, 27 ga watan Mayu.

An yi ganawar ne domin tattauna matsalar rashin tsaro, da yawan sace-sacen mutane musamman a yankin arewa maso yammacin kasar.

Gwamna Masari ya nemi a daina biyan masu garkuwa kudin fansa

Gwamna Masari ya nemi a daina biyan masu garkuwa kudin fansa
Source: UGC

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa Buhari ya sake bayar da tabbaci na jaddada tsayuwar dakan sa wajen samar da ingantaccen tsaro a fadin kasar nan.

Furucin shugaban kasa Buhari na zuwa ne yayin ganawar sa da kungiyar gwamnonin Arewa cikin babban dakin taro na Council Chambers dake fadar Villa a garin Abuja.

Gwamnonin da suka halarci taron a fadar shugaban kasa sun hadar da Abdulaziz Yari (Zamfara), Kashim Shettima (Borno), Nasir El-Rufa'i (Kaduna), Aminu Bello Masari (Katsina), da kuma Aminu Waziri Tambuwal (Sakkwato).

KU KARANTA KUMA: Zan kawo karshen masu garkuwa da mutane da 'yan bindiga - Buhari ya fadawa gwamnoni

Sauran gwamnonin da a halin yanzu suke tsaka da ganawa da shugaba Buhari sun hadar da; Muhammad Baduru Abubakar (Jigawa), Yahaya Bello (Kogi), Atiku Bagudu(Kebbi), Simon Lalong (Filato), da kuma Abubakar Sani Bello (Neja).

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel