Kotu ta aika sammaci ga kwamishinan yan sandan Niger kan rashin kama tsohon gwamna Aliyu da Nasko

Kotu ta aika sammaci ga kwamishinan yan sandan Niger kan rashin kama tsohon gwamna Aliyu da Nasko

Wata babbar kotun Tarayya dake Minna a ranar Litinin, 27 ga watan Mayu ta umurci kwamishinan yan sandan jihar Niger da ya gurfana a gabanta, sannan ya bada jawabi akan rashin aiwatar da umurninta na kama tsohon gwamna Babangida Aliyu da Umar Nasko.

Justis Aminu Aliyu ya umurci kwamishinan yan sanda da ya gurfana tare da masu laifin guda biyu a ranar 13 ga watan Yuli.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ta rahoto cewa Aliyu da Nasko sun kai lokacin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), ta bayar don gurfana a kotu a ranar 23 ga watan Mayu bisa zargin karkatar da kudi kimanin N1.9bn amman suka gaza bayyana, wanda hakan yayi sanadiyar da justice Aliyu ya bada umurnin kamo su.

Kotu ta aika sammaci ga kwamishinan yan sandan Niger kan rashin kama tsohon gwamna Aliyu da Nasko

Kotu ta aika sammaci ga kwamishinan yan sandan Niger kan rashin kama tsohon gwamna Aliyu da Nasko
Source: Depositphotos

A lokacin da lamarin ya taso, Aliyu da Nasko sun gaza bayyana, lawyan tsohon gwamna Olajidele Ayodele, SAN, ya halarci zaman kotun.

Ayodele, har ila yau, yace zai tabbatar da cewa ya sanar da tsohon gwamnan akan kwanan watan da za a sake zama.

KU KARANTA KUMA: HDP ta bukaci kotun koli da ta hana rantsar da Buhari

A bangaren shi, mai shari’a, Olumuyiwa Akinbori, SAN, ya bayyana mamaki akan rashin bayyanan mai laifin ba tare da wani kwakkwarar dalili ba.

An daga sauraran karan zuwa ranar 13 ga watan Yuli.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel