Barayin yan Najeriya za su far mun bayan 2023 - Buhari

Barayin yan Najeriya za su far mun bayan 2023 - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 27 ga watan Mayu ya bukaci kotun kula da da’ar ma’aikata ta CCB, da ta adana takardar kaddamar da dukiyoyinsa da kyau, domin wadanda ke fuskantar tuhuma na cin hanci da rashawa a gwamnatinsa za su far masa bayan ya sauka daga mulki.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a lokacin da shi da mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo suka karbi sabon fam din kaddamar da dukiya daga Shugaban CCB, Farfesa Mohammed Isa, wanda ya jagoranci tawagar ciki harda Barista Murtala Kankia da Dr. Emmanuel Attah a fadar Shugaban kasa, Abuja.

Shugaban kasar a jawabinsa yace: “Nayi farin ciki da kasancewarku a nan, Ina baku tabbacin cewa zanyi gaggawan cike wannan fam din sannan na dawo dashi gare ku saboda a karshen 2023, na san cewa akwai mutane da dama da za su so zamar dashi hujja a gaare ni.

Barayin yan Najeriya za su far mun bayan 2023 - Buhari

Barayin yan Najeriya za su far mun bayan 2023 - Buhari
Source: Depositphotos

“Saboda haka dan Allaj ku tabbatar kun adana shi da kyau saboda akwai mutanen da suke ganin bai kamata a tuhume su ba amma kuma aka tuhume su sannan yanzu haka wasun sun a cikin matsala.

KU KARANTA KUMA: HDP ta bukaci kotun koli da ta hana rantsar da Buhari

“Ina sanya ran za su ake ni sannan kuma wannan nan ne daya daga cikin makaman. Don haka ina fatan za ku ajiye shi.”

Ya bayyana cewa wannan ne karo na farko da yake ganin kungiyar tun bayan nadinsu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel