HDP ta bukaci kotun koli da ta hana rantsar da Buhari

HDP ta bukaci kotun koli da ta hana rantsar da Buhari

Jam’iyyar Hope Democratic Party (HDP) ta daukaka kara a gaban kotun koli kan ta hana rantsar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 29 ga watan Mayu.

HDP ta daukaka karan ne inda ta nemi a soke hukuncin kotun sauraron karar zaben Shugaban kasa karkashin jagorancin Justis Joseph Ikyegh wanda a ranar 22 ga watan Mayu, ya ki amincewa da bukatar hana rantsar da Buhari.

HDP da dan takararta, Ambrose Owuru, na daga cikin jam’iyyun siyasa da ke kalubalantar sakamakon zaben Shugaban kasa na ranar 23 ga watan Fabrairu.

HDP ta bukaci kotun koli da ta hana rantsar da Buhari

HDP ta bukaci kotun koli da ta hana rantsar da Buhari
Source: Facebook

Jam’iyyar na rokon kotun koli da ta hana zababben Shugaban kasar daga gabatar da kanshi a bikin rantsarwa a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu har zuwa lokacin da za a yanke hukuncin karshe na kalubalantar zabensa.

KU KARANTA KUMA: Babu adalci a hukunci da kotu ta yanke a jihar Zamfara - Adams Oshiomhole

A karar da Yusuf Ibrhim ya daukaka a madadinta, HDP na rokon wani umurni na kotun kolin da ke umurtan Shugaban majalisar dattawa ko Shugaban alkalan Najeriya da su ci gaba da jan ragamar mulki har zuwa loacin da za a daidaita komai na zaben da ya gabata.

Musamman, jam’iyyar tayi ikirarin cewa kotun zaben ta ki amfani da sashi na 25 na dokar zaben, 2019 wanda ya bukaci dakatar da bikin rantsarwa har zuwa lokacin da kotun za ta yanke hukunci kan sahihancin zaben.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel