Zan kawo karshen masu garkuwa da mutane da 'yan bindiga - Buhari ya fadawa gwamnoni

Zan kawo karshen masu garkuwa da mutane da 'yan bindiga - Buhari ya fadawa gwamnoni

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa tana aiki babu kama hannun yaro domin kawo karshen garkuwa da mutane da hare-haren da 'yan bindiga ke kaiwa a wasu sassan kasar.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin ganawa da ya yi da wasu gwamnonin jihohin arewa a fadarsa da ke Abuja. An kira taron ne domin tattauna kallubalen tsaro da ke adabar wasu jihohin.

Gwamnonin da suka kai ziyarar karkashin Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara sun yiwa shugaba Buhari bayani kan halin tsaro a jihohinsu.

Zan kawo karshen masu garkuwa da mutane da 'yan bindiga - Buhari ya fadawa gwamnoni

Zan kawo karshen masu garkuwa da mutane da 'yan bindiga - Buhari ya fadawa gwamnoni
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Gwamna Ganduje ya nada sabbin manyan sakatarori 36 (sunaye)

Bayan Yari sauran gwamnonin da suka hallarci taron sun hada da Kashim Shettima na jihar Borno, Simon Lalong na Jihar Filato Plateau, Yahaya Bello na jihar Kogi, Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, Aminu Bello-Masari na jihar Katsina da Aminu Tambuwal na jihar Sokoto.

Sauran sun hada da Gwamna Muhammad Abubakar Badaru na jihar Jigawa, Atiku Bagudu na jihrar Kebbi da Abubakar Sani-Bello na jihar Niger.

"Ina sane da halin kallubalen tsaro da kasar ke ciki a kowanne lokaci. Ina samun rahotanni da kowane rana da mako. Na saurari rahotannin ku.

"Zan duba shawarwarin da suka bayar. Ina sane da abinda ke faruwa amma a yau na sake samun karin haske."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel