Shirin horar da yara miliyan uku a arewa ba ta da alaka da almajirai - Bishop Kukah

Shirin horar da yara miliyan uku a arewa ba ta da alaka da almajirai - Bishop Kukah

Bishop din mujami'ar Kotolika na jihar Sokoto, Matthew Hassan Kukah ya ce ba zai fasa shirin sa na bayar da tallafin ilimi ga kananan yara miliyan 300 a arewa ba kuma ba ta da alaka da almajirai.

Ya yi wannan jawabin ne ranar Litinin a Abuja a Kukah Center tare da hadin gwiwar ProFuuro wurin kaddamar da dakunnan karatu na zamani domin makarantun frimare na jihohin arewa.

Kukah Center ta ce za ta inganta ilimin dalibai miliyan biyu zuwa uku cikin shekaru biyar masu zuwa.

Shirin bawa yaran arewa 3m tallafi ba na almajirai bane - Bishop Kukah

Shirin bawa yaran arewa 3m tallafi ba na almajirai bane - Bishop Kukah
Source: UGC

DUBA WANNAN: Gwamna Ganduje ya nada sabbin manyan sakatarori 36 (sunaye)

Jagoran shirin, Micheal Magaji wanda ya wakilci Kukah ya shaidawa manema labarai cewa za a kaddamar da shirin a jihohin arewa 12 kuma daliban frimare 123,000 da malamai 5,000 ne za su amfana cikin karo na farko a shirin.

Magaji ya ce shirin ba ta da wani alaka da almajirai kamar yadda Shugaban kungiyar, Muslim Rights Concern (MURIC), Ishaq Akintola ya yi ikirari.

Da farko, Shugaban Kukah Centre, Rabarand Fada Atta Barkindo ya ce ba gaskiya bane cewa ana shirin sauya almajirai miliyan 10 zuwa kiristanci.

A baya, Legit.ng ta ruwaito cewa Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta yi watsi da shirin tallafi na Rev. Matthew Kukah da zai horar da yaran Almajirai miliyan goma a yankin arewacin Najeriya.

A wata sanarwa da ya saki a ranar Laraba, 2 ga watan Janairu, Daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya bayyana cewa kudirin Rev.

Kukah akan haka na tattare da alamar tambaya. A cewarsa wannan bukata ta Kukah yunkuri na son wa’azantar da yaran ga addinin Kirista, da kuma shirin yin mulkin mallakar zamani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel