Ma’aikatan Ogun sun yi wa Gwamna Allah ya isa kan rashin biyan kudi

Ma’aikatan Ogun sun yi wa Gwamna Allah ya isa kan rashin biyan kudi

Jaridar Punch ta rahoto cewa kungiyar kwadagon Najeriya ta reshen jihar Ogun ta bayyana cewa za ta bar gwamna Ibikunle Amosun mai shirin barin kan gadon mulki da hukuncin Ubangiji.

Shugaban NLC na jihar Ogun, Emmanuel Bankole yace sun hakura ta fawwalawa Allah komai bayan gwamnan ya ki biyan su bashin albashi da kudin sallama da wasu tarin alawus da ake bin sa.

Kwamared Bankole a madadin kungiyar ma’aikatan, yake cewa gwamna mai-jiran-gado watau Dapo Abiodun ya shirya karbar gadon wasu makudan bashi daga hannun gwamnatin Ibikunle Amosun.

Shugaban hukumar NLC na jihar ya bayyana wannan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a sakatariyar jihar Ogun. Bankole ya kira ‘yan jaridar ne domin fayyace halin da ma’aikata ake ciki.

KU KARANTA: Sabon Gwamnan APC ya tanadi ayyukan da zai yi kafin ya shiga ofis

Kungiyar take cewa maganar cewa gwamnatin Ogun ba ta bin ma’aikata bashin kudi kamar yadda ake rayawa, sam ba gaskiya bane. NLC tace akwai kudin su da ya makala a hannun gwamnan har yau.

“Mun dade mu na jiran Amosun ya cika alkawarin da yayi, na biyan mu bashin kudin mu na sallama fansho, cikon albashi, alawus din hutu da kuma kudin da ake rika zaftarewa daga albashi”

“Ko da cewa gaskiya ne an biya wasu daga cikin ma’aikata wannan kudi, sai dai har yanzu ba a biya da-dama daga cikin ma’aikatan kananan hukumomi da ma’aikatan makaranta kudin na su ba…”

A karshe shugaban ‘yan kwadagon yake cewa:

“Ko da babu abin da za mu iya yi a yanzu, na jefa mu cikin halin ha’ula’i da aka yi, mun kyale ka, mun bar ka da Allah!’

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel