Satar $40m: Babu hujjar da ke nuna Robert Azibaola yana da laifi - Kotu

Satar $40m: Babu hujjar da ke nuna Robert Azibaola yana da laifi - Kotu

Wani babban kotun tarayya da ke zama a Abuja ya wanke Robert Azibaola daga zargin da hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa yi masa na awon gaba da wasu kudi.

EFCC tana zargin Robert Azibaola da satar kudi har Dala miliyan 40. A karshe dai an karkare wannan shari’a inda Alkali yace babu wata hujja da ke nuna cewa wanda ake zargi ya aikata wannan laifi.

Alkali mai shari’a Nnamdi Dimgba yake kuma cewa ya kamata ace hukumar EFCC ta kawo Sambo Dasuki a matsayin shaida da zai taimaka wajen kafa hujja a kan zargin da ke kan Robert Azibaola.

KU KARANTA: Buhari zai yi wurgi da kudirin sauke shugaban Hukumar EFCC

Babu hujjar da ke nuna Robert Azibaola yana da laifi - Kotu

Azibaola: Kotu ta fatattaki karar EFCC bayan ta gaza kaffa hujja
Source: Depositphotos

Alkalin yake cewa:

“EFCC ta gaza kafa hujja daga ofishin mai ba shugaban kasa shawara a kan sha’anin tsaro.”

“Wanda yake kara bai iya gamsar da kotu cewa wanda ake tuhuma ya aikata wadannan laifi 2 da ake kararsa”

“Hukumar EFCC da mai kara su na neman su fi wanda ake tuhuma kokawa da shari'a.”

A karshe Alkalin yake cewa:

“Kotu ta saki Robert Azibaola bayan an gaza samun sa da laifin satar Dala miliyan 40, don haka yana da gaskiya a gaban shari’a.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel