Zan zarce tare da wasu daga cikin ministocina, inji Buhari

Zan zarce tare da wasu daga cikin ministocina, inji Buhari

-Shugaba Muhammadu Buhari yace akwai yiwuwar wasu daga cikin ministocinsa zasu koma aikinsu a zangonsa na biyu.

-Wasu daga cikin ministocin Buhari zasu cigaba da kasancewa cikin gwamnatinsa kamar yada shugaban ya fadi a hirar da yayi da gidan talabijin na NTA ranar Litinin.

A ranar Litinin yayin wata hira ta kai tsaye da gidan talabijin na kasa wato NTA tayi da shugaba Muhammadu Buhari, ya fadi cewa akwai yiwuwar wasu daga cikin ministocinsa zasu cigaba da aiki a zangonsa na biyu.

Shugaban ya fadi a hirar cewa yayin da wa’adin mulkinsa yazo karshe ya umurci ministoci da su kawo masa rahoton ayyukan da sukayi tsawon shekaru hudu a ofis. A daidai lokacin da ake sa ran mika wannan rahoto zai kasance na yin murabus ne daga aikin na su, amma shugaban yace “ wasu daga cikinsu kan iya cigaba da aikin”.

Wasu daga cikin ministocina zan zarce tare dasu, inji Buhari

Wasu daga cikin ministocina zan zarce tare dasu, inji Buhari
Source: Twitter

KU KARANTA:EFCC taki cewa komi kan zargin da ake yiwa Tinubu

Shugaban kasar ya nemi ko wane ministan da ya kawo rahotonsa tun farkon makon nan, kana kuma su fara shirye-shiryen barin ofis.

Shugaban ya kara da cewa zai mayar da hankalinsa a bangaren tsaro ne a wa’adinsa na biyu, musamman abinda ya shafi ‘yan sanda da kuma ma’aikatar shari’a domin ya tabbatar da hukumomin suna yin aikin da yakamata.

Mutane da dama sunyi ta korafe-korafe akan gazawar shugaban kasar wajen samar da wadataccen tsaro na rayuka da dukiyoyin jama’a. Boko Haram tayi nasarar hallaka daruruwan jami’an sojin Najeriya daga watan Yulin 2018 zuwa yanzu.

Kazalika, mutane sunyi korafi akan hukumar ‘yan sanda a dalilin gazawarta wurin magance matsalolin garkuwa da mutane, fashi da makami da kuma sauran miyagun laifuka da ake addabar sassa da dama na kasar nan a halin yanzu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel