Babu adalci a hukunci da kotu ta yanke a jihar Zamfara - Adams Oshiomhole

Babu adalci a hukunci da kotu ta yanke a jihar Zamfara - Adams Oshiomhole

- Shugaban jam'iyyar APC ya ce babu adalci ko kadan a hukuncin da kotu ta yanke a jihar Zamfara

- Ya ce daga yaya za a cusawa mutane dan takarar da bashi su,a zaba ba domin ya mulke su

Jiya Litinin ne shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Comrade Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa babu adalci a hukuncin da kotun koli ta yanke na bai wa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kujerar gwamnan jihar Zamfara, sannan kuma ta bata dukkanin kujeru 3 na majalisar dattawa, da kujeru 7 na majalisar wakilan tarayya da kuma kujeru 24 na majalisar jiha.

Oshiomhole, wanda wani dan jarida yayi masa tambayar, ya ce babu adalci a hukunci da kotun ta yanke ko kadan.

Babu adalci a hukunci da kotu ta yanke a jihar Zamfara - Adams Oshiomhole

Babu adalci a hukunci da kotu ta yanke a jihar Zamfara - Adams Oshiomhole
Source: Depositphotos

Ya ce, "Daga yaya zaka yi mini tambayar yadda nake ji, bayan mutanen jihar Zamfara sun zabe mu, amma kotu ta zo ta ce dukkanin wannan kuri'un sun tashi a banza.

"Bayan kuma lokacin da ake kada kuri'a, kotu ta tabbatar da cewa dan takarar mu bashi da matsala.

"Babu adalci a shari'a wurin cusawa mutane dan takarar da bashi suke so ba.

KU KARANTA: An kashe mutane 5, an kone gidaje 12 a wani rikici da ya barke a Jos

"Idan har kotu tana ganin cewa abinda muka yi ba daidai bane, mai yasa baza ta nemi a sake gabatar da zabe ba. Babu adalci ko kadan wurin kawo wanda mutane basu san shi ba ace ya mulke su. Amma abinda muka fahimta shine bayan kotun koli babu wata kotu da zaka iya zuwa sai dai ka jira hukuncin Allah. Saboda haka dole zamu yiwa kotun koli biyyaya. Amma abinda aka yi a Zamfara ba adalci bane ko kadan," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel