An kashe mutane 5, an kone gidaje 12 a wani rikici da ya barke a Jos

An kashe mutane 5, an kone gidaje 12 a wani rikici da ya barke a Jos

- Wani rikici da ya barke a Jos ranar Lahadin nan yayi sanadiyyar mutuwar mutane biyar

- Rikicin ya samo asali bayan tsintar gawar wani yaro a wata unguwa

Jiya Litinin ne rundunar 'yan sandan jihar Filato ta tabbatar da cewar an kashe mutane biyar an kuma kone gidaje 12 a wani rikici da ya barke a garin Jos ranar Lahadi.

Rikicin ya samo asali ne bayan an samu gawar wani yaro a tsakanin Anguwan Damisa da Dutse Uku, hakan ya janyo zanga zanga a yankunan Rikkos, Cele Bridge, Tina Junction da kuma Anguwan Rukuba dake arewacin Jos.

An kashe mutane 5, an kone gidaje 12 a wani rikici da ya barke a Jos

An kashe mutane 5, an kone gidaje 12 a wani rikici da ya barke a Jos
Source: UGC

Matasan sun shiga kaiwa mutane hari, suna fasawa mutane ababen hawa, suna kunnawa gidaje wuta. Zuwan jami'an tsaro gurin sYahine ya kwantar da tarzomar, sai dai kuma mun samu rahoton cewa an ji karar harbin bindiga cikin dare a yankin da lamarin ya auku.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar DSP Tyopev Terna ya bayyana sunan gawar yaron da aka samu da Enoch, sannan an kai gawar babban asibitin jihar.

KU KARANTA: Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: 'Yan Boko Haram sun yiwa mutane bakwai yankan rago a Maiduguri

Ya ce da taimakon jami'an tsaron jihar, sun kawo karshen rikicin, yanzu haka dai jami'an tsaro suna ta faman zirga zirga a yankin.

Sannan mun samu rahoton cewa wata kungiyar mata sun gabatar da zanga zanga jiya Litinin da safe, a kokarin da suke na hana jami'an tsaro kama su.

An bayyana cewa an kama matan inda aka loda su a motar sojoji a wata unguwa da ake kira da 'Executive Mansion' a kusa da Tina Junction.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel