Na raina irin kishin-kasar Saraki da Dogara a Majalisa inji Shugaba Buhari

Na raina irin kishin-kasar Saraki da Dogara a Majalisa inji Shugaba Buhari

A jiya Litinin 27 ga Watan Mayu ne shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya nuna rashin amannan sa da irin shugabancin Bukola Saraki da kuma Yakubu Dogara a majalisar tarayyar Najeriya.

Shugaban kasar ya koka da bata-lokacin da majalisa tayi wajen kammala aiki a kan kasafin kudin wannan shekarar. Buhari ya bayyana wannan ne a lokacin da yake magana da ‘yan jaridar NTA.

Buhari yake cewa majalisa ta gaji wata mummunar dabi’a na yin yadda ta ga dama, alhali kuwa masu rike da madafan iko ne za su ce ga yadda za ayi a gwamnati, sannan majalisa ta ke da ta cewa.

Shugaba Buhari ya bayyana wannan ne a lokacin da aka yi masa tambaya a game da kasafin kudin bana. Shugaban kasar yake cewa ‘yan majalisa ne su ke jawo bacin lokaci tamkar su su ka ajiye sa.

KU KARANTA: Ana kutun-kutun din tsige Magu daga Shugaban EFCC kafin kafa sabon gwamnati

Na raina irin kishin-kasar Saraki da Dogara a Majalisa inji Shugaba Buhari

Buhari ya taba tinkarar shugabannin majalisar gar-da-gar a kan kasafin kudi
Source: Twitter

“Na tambaye su ya su ke ji idan su ka sa Najeriya tayi cak na watanni 7 a dalilin sun ki sa hannu a kan kasafin kudin kasar. Sai dai ba ni su ke yi wa ba, Najeriya gaba daya su kayi wa illa…”

…Saboda haka idan ana maganar kishin-kasa, gaskiya ba na kawo su a lissafi, ko kadan…”

Shugaban kasar yace babu yadda ya iya da majalisar a dokar kasa domin ya zama dole kundin kasafin kudin ya bi ta hannunsu.

“Babu yadda za ayi ku rike kasafin kudi na watanni 7 ba tare da wani dalili ba. Idan har kun damu da Najeriya a ran ku…”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel