Sanatoci 51 na bayan Ahmad Lawan, yan majalisa 191 na bayan Gbajabiamila

Sanatoci 51 na bayan Ahmad Lawan, yan majalisa 191 na bayan Gbajabiamila

Yayinda ake shirye-shiryen gudanar da zaben shugabannin majalisar dokokin tarayya a watan Yuni, sanata Ahmad Lawan da dan majalisa Femi Gbajabiamila na alfahari da wasu abokan aikinsu da sukayi alkawarin kada musu kuri'a.

Sanata mai wakiltan Oyo ta Arewa, Fatai Buhari, da zababben dan majalisan wakilai mai wakiltan Ibadan ta arewa, Musiliudeen Akinremi a ranar asabar sun bayyana cewa Sanata Ahmed Lawan da Femi Gbajabiamila na da isasshen goyon bayan da zai basu nasara a zaben.

Fatai Buhari wanda yake amsa tambayoyi daga yan jarida a Ibadan, ya ce 51 cikin zababbun sanatocin APC 66 sun rattaba hannunsa kan takardan cewa zasu zabi Sanata Ahmed Lawan a zaben shugabancin majalisar.

KU KARANTA: Ke duniya! Kalli Malamin dake yin luwadi da almajiransa, kuma yana bada hayarsu a Sakkwato

Kana Akinremi wanda yake jagorantan kungiyar yakin neman zaben Gbajabiamila a yankin kudu maso yamma, yayinda ya karbi bakuncin wasu mambobin a gidansa dake Ibadan yace suna da mambobi 191 da ke bayan Gbajabiamila

Yace: "A matsayina na shugaban sabbin zababbun yan majalisar yankin, wannan adadin ya keta yan APC saboda munada magoya baya daga wasu jam'iyyun adawa."

"Za mu cigaba da magana da abokan aikinmu daga yankunnan kasar nan shida. Ina maka alkawari, Gbajabiamila na iya takara babu abokin hamayya. Munada tabbacin goyon bayana sama da mambobo 200 inda muka dawo 11 ga Yuni."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel