Kuma dai! Yan bindiga sun kuma kai mumunan hari kauyukan Katsina 2

Kuma dai! Yan bindiga sun kuma kai mumunan hari kauyukan Katsina 2

- Har yanzu, hare-haren yan bindiga a jihar Katsina bai tsaya ba

- Bayan umurnin shugaba Buhari, yan barandan sun sake kai wani hari

A daren Lahadi, wasu yan bindigan da suka addabi jihar Katsina sun kuma kai har kauyukan Batsari biyu inda akalla mutum daya ya rasa rayuwarsa kuma da dama sun jikkata.

Wadannan kauyuka da abu ya shafa sune Gobirawa da Biya-ka-Kwana.

An bayyana sunan mutumin da aka kashe a kauyen Biya-ka-Kwana matsayin Bilya Lawal. Kana majiyarmu ta bayyaca cewa yan barandan sun kora dabbobin jama'an .

Game da cewar mazauna garin, yan bindigan sun kai hari ne misalin karfe 10 na dare. Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya tabbatar da wannan labari.

KU KARANTA: Boko Haram sun bukaci Jonathan da ya Musulunta, sun aika masa da wata wasika - Clark

A wani labarin mai kama da haka, Masarautar garin Katsina ta fitar da wata muhimmiyar sanarwa, inda a cikin sanarwar ta aika da sakon ta'aziyya ga dukkanin al'ummar jihar akan ibtila'in da ya faru na kashe mutanen garin Batsari, Dan Musa, Kankara da Wagini da sauran garuruwa da lamarin ya shafa.

Sakataren masarautar garin Katsinan Alhaji Bello M IFO shine ya fitar da sanarwar, inda ya shaidawa al'umma cewa sakamakon yanayin da al'ummar jihar suka tsinci kansu na jimami da alhini, masarautar ta yanke shawarar ba zata gabatar da hawan sallah ba a wannan karon.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel