Jihar Kano: Za'a damke mukarraban sarkin Kano 3

Jihar Kano: Za'a damke mukarraban sarkin Kano 3

Hukumar amsa korafe-korafe da yaki da rashawan jihar Kano tana shirin garkame shugaban ma'aikatan sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, Alhaji Munir Sanusi, kan rashin gurfana gaban hukumar domin amsa tambayoyi.

Kana za'a damke wasu ma'aikatan masarautar Kano biyu, Mujitaba Abba Sani da Sani Muhammad Kwaru, wadandan sukayi kunnen kashi kan gayyatar da hukumar domin amsa tambayoyi kan zargin da ake yiwa sarkin Kano na badakalar N4bn.

Hukumar ta shirya tsaf domin shigar da kara kotun Majistare a yau domin samun ikon damkesu, wani majiya a hukumar ya laburta.

A labari mai kama da haka, Gammayar kungiyar yan Arewa masu rajin samar da cigaba da dimukradiyya, NADP ta soki lamirin mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II, inda ta nemi yayi gaggawar yin murabus daga sarautar Kano don kare mutuncin masarautar.

KU KARANTA: Ke duniya! Kalli Malamin dake yin luwadi da almajiransa, kuma yana bada hayarsu a Sakkwato

Kungiyar ta bayyana haka ne a ranar Alhamis, 23 ga watan Mayu a karshen taronta daga gudanar a babban birnin tarayya Abuja, taron daya samu halartar wakilanta daga jahohi 18 a Arewacin Najeriya inda suka tattauna batun matsalar tsaro a Arewa da kuma rikicin masarautar Kano.

Haka zalika kungiyar ta jinjina ma namijin kokarin da gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje yayi na nada sabbin sarakunan gargajiya guda hudu masu daraja ta daya a jahar Kano, na Rano, Bichi, Karaye da Gaya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel