Zan karfafi ‘yan sanda da ma’aikatar shari’a, inji Buhari

Zan karfafi ‘yan sanda da ma’aikatar shari’a, inji Buhari

-Tattaunawar da akayi da shugaba Buhari na nuna cewa a wa'adinsa na biyu masu laifi baza su samu wani rangwame ba musamman saboda kiransa da akeyi da sunan 'Baba go-slow shi kuwa ya lashi takobin ba wadannan mutane mamaki.

Shugaba Muhammadu Buhari a jiya yace zai karfafawa jami’an yan sanda da kuma ma’aikatar shari’a gwiwa domin kawo karshen matsalolin kasar nan a wa’adinsa na biyu.

Da yake magana jiya yayin wata tattaunawa ta musamman da akayi da shi kai tsaye a gidan talabijin na kasa wato NTA, shugaban yace duk wanda ke neman ya kawo tangarda a cikin binciken zai fuskanci hukunci.

Zan karfafi ‘yan sanda da ma’aikatar shari’a, inji Buhari

Zan karfafi ‘yan sanda da ma’aikatar shari’a, inji Buhari
Source: Twitter

KU KARANTA:EFCC taki cewa komi kan zargin da ake yiwa Tinubu

Shugaban kasar dai za’a rantsar da shi ne a karo na biyu gobe a filin Eagle square dake Abuja. Da yake amsa tambaya akan ko za’a samu wani sassauci daga bangarensa a wa’adi na biyu, cewa yayi: “ Duk masu kirana da Baba go-slow zasu gani ko ni Baba go-slow ne, saboda zan sa yan sanda da ma’aikatar shari’a su dada tsauri.

“ Idan kuma na fahimci cewa ba suyi tsauri ba, zanyi kokarin gano wanda keda sa hannu wurin kawo tsaikon. Tabbas nasan sabon babban sufeton yan sanda ba zai iya aikin ba shi kadai dole sai da goyon bayan kwamishinoni da wasu manyan kwamandodinsa.

Akan wakar shahararraren mawakin arewacin Najeriya nan mai suna Dauda Rarara da yake gargadin barayi da cewa su gudu, shugaba yace, “ To ko dai su tsaya suyi abinda ya dace ko kuma su gudu.” Inji Shugaba Buhari.

Ya sake jaddada kudurinsa na sanya yan sanda da sashen shari’a tsayuwa a tsaye bisa kafafunsu domin daidaita al’amuran kasa.

“ Yan sanda sune kan gaba wurin fada da miyagun ayyuka a al’umma. Babu yankin da bai da tashar ‘yan sanda a don haka na nemi su zage dantse wajen yaki da muggan laifuka.” A cewarsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel