Sarkin Kano ya halarci taron bude baki da Buhari ya shirya a fadar shugaban kasa

Sarkin Kano ya halarci taron bude baki da Buhari ya shirya a fadar shugaban kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shirya liyafar bude baki ga wasu zababbun manyan sarakunan gargajiya dake Najeriya a fadar gwamnati dake Aso Rock Villa a babban birnin tarayya Abuja.

Legit.ng ta ruwaito daga cikin manyan sarakunan da suka halarci liyafar akwai mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, Ooni na Ife Adeyey Enitan –Ogunwusi.

KU KARANTA: Babu aiki ranar Laraba saboda za’a rantsar da Buhari karo na biyu – Gwamnati

Sarkin ya halarci taron bude baki da Buhari ya shirya a fadar shugaban kasa

Sarkin ya halarci taron bude baki da Buhari ya shirya a fadar shugaban kasa
Source: UGC

Sauran sun hada da mai martaba Etsu Nupe Alhaji Yahaya Abubakar, Tor Tiv James Ayatse da sauran manyan sarakunan gargajiya daga yankin kudu masu kudanci da kuma kudu maso gabashin Najeriya.

Haka zalika a taron an hangi keyar wasu daga cikin manyan jami’an fadar shugaban kasa kamarsu shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari, da wasu hadimai yan gaban goshin shugaba Buhari.

A wani labarin kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya danganta gaskiya da rikon amana da yan Najeriya suka ganin yana dashi ga horon daya samu a wajen Malaman da suka koyar dashi da sa’anninsa a makarantar Firamari data sakandari a zamaninsu.

Buhari ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi ta musamman a daren Alhamis da gidan talabijin na NTA, inda yace Malamansu sun basu horo ta yadda idan kayi abin kirki zasu yaba maka idan kuma kayi na tsiya zasu hukuntaka a gaban kowa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel