Yadda na ceci raina da kyar a mazabata - Sanata

Yadda na ceci raina da kyar a mazabata - Sanata

- Sanata Monsurat Sunmonu ta bayyana yadda tasha da ranta da kyar a hannun fusatattun matasan yankin da take wakilta

- Sanatar ta yi bayanin ne a lokacin da take gaabatar da wani aiki da ta yi a karamar hukumar Egbede

Jiya Litinin ne Sanata mai wakiltar jihar Oyo ta tsakiya a majalisar tarayya, Sanata Mosurat Sunmonu, ta bayyana yadda mutanen garin Ibadan suka biyo su ita da 'yan tawagar ta da adduna, da muggan makamai, akan zargin da suke yi na cewa ta kasa cika musu alkawuran da ta dauka a lokacin yakin neman zabe.

Sanatar, wacce ta wakilci jihar Oyo na tsawon shekaru hudu, kuma ita ce mace ta farko da ta fara rike mukamin kakakin majalisar jihar. Ta ce dakyar ta sha da raina daga hannun fusatattun mutanen a lokacin da take yawon neman kamfen a Oke Ayotuntun dake garin Oki, cikin karamar hukumar Egbede jihar Oyo.

Yadda na ceci raina da kyar a mazabata - Sanata

Yadda na ceci raina da kyar a mazabata - Sanata
Source: Facebook

Sanatar ta bayyana hakan ne a lokacin da take gabatar da wani aiki na magance zaizayar kasa a Oke Ayotuntun dake Oki.

Aikin wanda ya hada da kwalbati, gadoji da kuma hanya mai tsawon kilomita 3.3, Sanata Monsurat Sunmonu ta gabatar da su, sannan kuma an biya kudin aikin taga ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.

Sanatar wacce ta samu tarba ta musamman ga al'ummar yankin, ta bukaci mutane da su dinga nunawa wakilansu laifin da suke yi, wurin tunasar da su akan irin alkawuran da suka dauka lokacin yakin neman zabe.

KU KARANTA: Hukumar zabe ta bayyana sunayen 'yan takarar da suka lashe zabe a jihar Zamfara

Ta bayyana cewa shekaru hudun da tayi a matsayin Sanata mai wakiltar jihar Oyo ta tsakiya a majalisar tarayya, wata dama ce da ta samu domin gabatar da ayyukan babbar hanyar Oyo zuwa Ogbomoso, da kuma kammala aikin magance zaizayar kasa a yankin Oke Ayotuntun.

A bayanin sa, shugaban kasa Muhmmadu Buhari, wanda Ministan Lafiya, Farfesa Isaac Adewole ya wakilta, ya bayyana cewa babu tantama aikin zai kawowa al'ummar yankin sauyi.

Ya kuma kara da cewa aikin yana daya daga cikin ayyuka 19 da gwamnatin tarayya ta sanya hannu zata yi domin magance matsalar zaizayar kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel