Zan bawa masu kira na 'Baba Go slow' mamaki a zango na biyu - Buhari

Zan bawa masu kira na 'Baba Go slow' mamaki a zango na biyu - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar zai bawa masu kiransa da 'Baba Go slow' mamaki a zangon mulkin sa na biyu da zai fara ranar Laraba mai zuwa.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne yayin hira ta musamman da aka yi da shi a daren ranar Litinin.

Da yake amsa tamabaya a kan zargin da wasu ke yi na cewar gwamnatinsa na tafiyar hawainiya, sai shugaban kasar ya bayyana cewar al'amura zasu fi gudana ba tare da bata lokaci ba a zangon mulkinsa na biyu.

Da yake magana a kan alakar sa da bangaren majalisa, Buhari ya ce: "na kira da Saraki da Dogara kuma na fada musu cewar kasa suke yiwa illa ba ni ba, babu wani uzuri da majalisa zata gabatar a kan rike kasafin kudi har tsawon wata 7.

Zan bawa masu kira na 'Baba Go slow' mamaki a zango na biyu - Buhari

Buhari
Source: Twitter

"Na tambayi Dogara da Saraki menene ribar su idan sun hana al'amura gudana wa a gwamnatina, bana ganinsu a cikin masu kishin kasa."

DUBA WANNAN: Muhimman abubuwa 10 da Buhari ya fada yayin hira da shi

A kan nadin sabbin ministoci da wadanda zai nada domin taya shi mulki a zango n biyu, shugaba Buhari ya ce bai tattauna kunshin mutanen da zai nada ba da kowa ba.

"Na riga nayi taro na karshe da majalisar zartarwa da na kafa, ban kuma tattauna da kowa ba a kan sabbin nade-naden da zan yi a zangona na biyu ba," a cewar Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel