Babu aiki ranar Laraba saboda za’a rantsar da Buhari karo na biyu – Gwamnati

Babu aiki ranar Laraba saboda za’a rantsar da Buhari karo na biyu – Gwamnati

Gwamnatin tarayya ta sanar da bada hutu a ranar Laraba, 19 ga watan Mayu don murnar rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu, kamar yadda babban sakatariyar ma’aikatan cikin gida, Georgina Ehuriah ta bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ehuriah ta sanar da haka ne a ranar Litinin, 27 ga watan Mayu, inda tace a madadin ministan al’amuran cikin gida, Abdulrahman Dambazau, yana taya shugaban kasa Buhari samun nasara a karo na biyu.

KU KARANTA: Murnar cika shekaru 88: Buhari ya jinjina ma Aminu Alhassan Dantata

Babu aiki ranar Laraba saboda za’a rantsar da Buhari karo na biyu – Gwamnati

Yayin karbar rantsuwa karo na 1
Source: Facebook

Haka zalika Dambazau yayi kira ga kafatanin yan Najeriya dasu baiwa gwamnatin Buhari goyon baya a bisa ayyukanta da tsare tsarenta, wanda ya bayyanasu a matsayin hanyoyin ciyar da Najeriya gaba da kyautata rayuwar dan Najeriya.

Ministan ya bada tabbacin idan har yan Najeriya sun baiwa Buhari goyon baya ba karamin cigaba za’a samu a Najeriya ba, ta yadda hatta kasashen duniya zasu dinga kishi da Najeriya.

Daga karshe minista Dambazau yayi fatan samun nasara ga gwamnati mai zuwa, tare da fatan Allah Yasa ayi taron rantsar da shugaban kasa lafiya a gama kuma lafiya.

Sai dai kodayake a ranar 29 za’a rantsar da Buhari, amma sai ranar 12 ga watan Yuni za’a gudanar da kayataccen bikin rantsarwar tare da gudanar da bikin sabuwar ranar dimukradiyya da gwamnatin Buhari ta kirkira don tunawa da zaben 1993 da marigayi Moshood Abiola ya lashe.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel