2023: Ko a siyasar ma ba kada wani galihu - Peter Obi ya yi kaca-kaca da Amaechi

2023: Ko a siyasar ma ba kada wani galihu - Peter Obi ya yi kaca-kaca da Amaechi

Dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Peter Obi, ya yi ikirarin cewa Ministan sufuri Rotimi Amaechi, ba ya da wata cancanta a fagen siyasa ta tsoma bakin kan yankin da kujerar shugaban kasa za ta karkata a zaben 2023.

Peter Obi

Peter Obi
Source: UGC

Peter Obi wanda ya kasance abokin takarar Atiku Abubakar yayin zaben shugaban kasa da aka gudanar a bana, ya ce Ministan sufuri baya da wani galihu a siyasance ko da kuwa a mahaifar sa ta jihar Ribas da za ta bashi damar tsoma baki kan yankin Najeriya da zai samar da shugaban kasa a 2023.

Da ya ke ganawa da manema labarai bayan halartar bikin kaddamar da wani littafi da aka gudanar a birnin Fatakwal domin karrama gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, Peter Obi ya bayyana mamakin yadda Amaechi ke rinjayar da kujerar shugaban kasa zuwa yankin Kudu maso Gabas duk da bai fito daga cikin yankin ba.

KARANTA KUMA: Rashin Tsaro: Tabbas aminci zai samu a Najeriya - Buhari

Cikin kalaman sa Peter Obi ya ce "Amaechi ba ya da hurumin da zai ari bakin al'ummar yankin Kudu maso Gabas ya ci masu Albasa. Ya ce ba bu wata gudunmuwa da ya bai wa jam'iyyar sa ta APC wajen samun nasara a zaben bana."

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Ministan sufuri a makon da ya gabata ya nemi al'ummar yankin Kudu maso Gabashin Najeriya da su dawo daga rakiyar hankoron kujerar shugaban kasa a zaben 2023 sakamakon rashin goyon bayan jam'iyyar APC a zaben bana.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel