FG ta fadi wasu bangarori 4 da zata samar da guraben aiyuka ga mutum miliyan 20

FG ta fadi wasu bangarori 4 da zata samar da guraben aiyuka ga mutum miliyan 20

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewar ta bullo da wasu dabaru da zasu bata damar kirkirar guraben aiyuka ga 'yan Najeriya mutum miliyan 20 daga bangaren noma, gine-gine, sufuri da wasu aiyuka na musamman, a zangonta na biyu, a cewar ministan ma'aikatar kamfanoni, fatauci da saka hannun jari, Mista Okechuwkwu Enelamah.

Enelamah ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Abuja yayin wani taro da masu ruwa da tsaki a kan samar da guraben aiyuka a gwamnatin tarayya.

Ministan ya samu wakilcin Mista Sunday Akpan, babban sakatare a ma'aikatar.

A cewar sa, ma'aikatar ta umarci sashen asusun bayar da horo (ITF) da ya bullo da wani gagarumin shiri da zai kawo karshen matsalar rashin aiki da ta dade tana damun kasar nan.

"ITF ta bullo da wasu dabaru da a cikin zangon gwamnati na biyu zasu samar da guraben aiki miliyan 20 daga banagarori guda hudu na tattalin arziki" a cewar Enelamah.

Ya bukaci masu ruwa da tsaki da su bijiro da wasu dabaru da zasu share hanyar habakar tattalin arziki ta hanyar samar da guraben aiyuka ga 'yan kasa.

A jawabinsa, babban darektan ITF, Mista Joseph Ari, ya ce batun yan Najeriya da basu da aiki ya dade yana damun gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya bayyana cewar hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta bayyana samun karuwar 'yan Najeriya marasa aiki daga mutum miliayn 17.6 a shekarar 2017 zuwa mutum miliyan 20.9 a sheakarar 2018.

Ya kara da cewa adadin marasa aikin na cigaba da karu wa duk da karin yawan guraben aiki da gwamnatin Buhari ta kirkira tun bayan zuwanta a shekarar 2015.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel