Tabbatar da tsaro: Gabanin rantsarwarsa karo na biyu, Buhari ya karbi takardar bayyana dukiyar da ya mallaka

Tabbatar da tsaro: Gabanin rantsarwarsa karo na biyu, Buhari ya karbi takardar bayyana dukiyar da ya mallaka

Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin shugaban cibiyar ladabin ma'aikatan gwamnati wato Code of Conduct Bureau CCB. Farfesa Muhammad Isa, a ranar Litinin, 27 ga wtaan Mayu, 2019.

Buhari ya karbi bakuncinsa ne a fadar shugaban kasa dake birnin tarayya Abuja tare Mista Emmanuel Attah, Murtala Aliyu Kankia da ministan shari'a, Abubakar Malami.

Tabbatar da tsaro: Gabanin rantsarwarsa karo na biyu, Buhari ya karbi takardar bayyana dukiyar da ya mallaka

Tabbatar da tsaro
Source: Twitter

Shugaban CCB ya kawo ma shugaba Muhammadu Buhari takardar cika dukiyoyin da ya mallaka daga lokacin da ya hau mulki a 29 ga Mayun 2015 zuwa yanzu kafin a sake rantsar da shi a karo na biyu.

Wannan tsari ne wanda ya wajaba a kan ma'aikatan gwamnati kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

KU KARANTA: A karon farko, Kogunan Gusau ya yi magana kan ibtila'in rasa kujerarsa

Rashin yin hakan ya jefa tsohon alkalin alkalai, Walter Onnoghen, cikin matsalan da ya kai ga tsigeshi a kwanakin baya.

Hadimin shugaban Buhari, Bashir Ahmed, ya bayyana cewa shugaba Buhari ya yi alkawarin cika takardar da wuri ba tare da bata lokaci ba.

Yace: Bayan karban takardan cike dukiyoyin da ya mallaka daga cibiyar, Shugaba Muhammadu Buhari yayi alkawarin cikawa da mayar da shi ba tare da bata lokaci ba."

Tabbatar da tsaro: Gabanin rantsarwarsa karo na biyu, Buhari ya karbi takardar bayyana dukiyar da ya mallaka

Tabbatar da tsaro: Gabanin rantsarwarsa karo na biyu, Buhari ya karbi takardar bayyana dukiyar da ya mallaka
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel