Korafin gwamnoni a kan hukumar NFIU ba ya da tushe - NULGE

Korafin gwamnoni a kan hukumar NFIU ba ya da tushe - NULGE

Kungiyar ma'aikatan kananan hukukomi ta Najeriya NULGE, ta nemi gwamnatin tarayya da tayi fatali da korafin gwamnoni akan shawarar hukumar nan dake bincike akan harkokin da suka hafi kudin kasa NFIU.

Hukumar NFIU dake gudanar da binciken sirri akan harkokin da suka shafi kudin kasar nan ta shawarci gwamnatin tarayya a kan aikawa kananan hukukomin kasar nan kudin su kai tsaye a madadin biyo da su ta hannun gwamnoni.

Wasu daga cikin gwamnonin Arewa

Wasu daga cikin gwamnonin Arewa
Source: Facebook

A sanadiyar wannan shawara gwamnonin Najeriya bisa jagorancin shugaban kungiyar su, gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari, a makon da ya gabata ya yi korafin cewa hukumar NFIU na yi masu kutse da shiga abin da babu ruwan ta.

Bayan jifan ta da sa ido, kungiyar gwamnonin Najeriya NGF, ta ce hukumar NFIU na yiwa gwamnonin kasar nan katsalandan da kuma shishshigi a kan kudaden kananan hukomomin jihohin su.

Kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi NULGE, ta nemi gwamnatin tarayya da ta yi fatali da wannan korafi na gwamnoni da a cewar ta ko kadan ba ya da tushe ballantana madogara ta gaskiya kamar yadda shugaban ta na kasa Kwamared Khalil Ibrahim ya bayyana a ranar Lahadi.

KARANTA KUMA: Abubuwa 5 da za su faru a wannan mako cikin Najeriya da Duniya baki daya

Ko shakka babu gwamnonin Najeriya sun bayyana takaicin su dangane da yadda hukumar NFIU ke neman kawo sabon tsari na haramtawa kudin kananan hukumomin kasar nan biyo wa ta hannun su.

A halin yanzu dai tuni hukumar NFIU bayan neman hadin gwiwar hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati ta EFCC, ta sanar tare da tsayar da ranar 1 ga watan Yuni domin fara aika wa kananan hukumomi kudin su kai tsaye.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel