Ba za mu iya alkawarin kawar da Boko Haram ba – Garba Shehu

Ba za mu iya alkawarin kawar da Boko Haram ba – Garba Shehu

- Babban hadimin Shugaban asa Buhar a kafofin watsa labarai, Garba Shehu yaace ba zai iya bayar da tabbaci ko Buhari zai kawo karshen yan ta’addan Boko Haram ko kuma akasin haka

- A cewarsa, ta’addanci babban kalubale ne da duniya baki daya ke fuskanta harma ga kasashe da suka ci gaba sosai da kuma makamai

- Sai dai kuma yace lallai gwamnatin tarayya na iya bakin kokarinta wajen magance matsalar fashi da makami da kuma sace-sacen mutane

Babu tabbacin ko gwamnatin Shugaban Muhammadu Buhari za ta kawo karshen ta’addancin Boko Haram da ya adabi Najeriya a cewar kakakin Shugaban kasa, Garba Shehu.

Shehu ya bayyana hakan ne yayinda yake jawabi a Sunrise Daily, wani shiri da Channels TV ke haskawa.

Ba za mu iya alkawarin kawar da Boko Haram ba – Garba Shehu

Ba za mu iya alkawarin kawar da Boko Haram ba – Garba Shehu
Source: Twitter

“Ba zan iya alkawarin cewa za a kawar da Boko Haram ko ba za a kawar da sub a amma ai kalubale ne da duniya baki daya ke fuskanta harda ga wadanda suka ci gaba sosai, da kakashe masu makamai, har yanzu kalubale ne,” inji Garba Shehu a lokacin da aka tambaye shi ko ta’addanci ya zo zama ne ko kuma za a kawar dashi baki daya.

KU KARANTA KUMA: Shugaban kasa Buhari ya gana da sarakunan kudu maso kudu a fadarsa

Sai dai kuma yace lallai gwamnatin tarayya na iya bakin kokarinta wajen magance matsalar fashi da makami da kuma sace-sacen mutane.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel