Boko Haram sun bukaci Jonathan da ya Musulunta, sun aika masa da wata wasika - Clark

Boko Haram sun bukaci Jonathan da ya Musulunta, sun aika masa da wata wasika - Clark

- Wani jigon kasa, Cif Edwin Clark, ya bayyana cewa yan ta’addan Boko Haram sun aika ma tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan wasika

- Clark yace kungiyar yan ta’addan ta bukaci tsohon shugaban kasar da ya musulunta a wasikan da aka aika mishi

- Har ila yau ya kara da cewa gazawan shugaban kasa Buhari wajen magance rashin tsaro a kasar ya kasance abun mamaki

Wani jigon kasa, Cif Edwin Clark, ya bayyana cewa yan ta’addan kungiyar Boko Haram sun aika ma Goodluck Jonathan wasika a lokacin da yake shugabancin kasa kan cewa ya musulunta.

Clark har ila yau yace gazawan shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen yakar matsalar tsaro cikin shekaru hudu da suka gabata abu ne mai matukar damuwa.

Jigon har ila yau ya kara da cewa yan ta’addan Boko Haram a kasar sun kasance da goyon bayan wasu manya daga cikin jami’an gwamnati da kuma manyan yan siyasa.

Boko Haram sun bukaci Jonathan da ya Musulunta, sun aika masa da wata wasika - Clark

Boko Haram sun bukaci Jonathan da ya Musulunta, sun aika masa da wata wasika - Clark
Source: Depositphotos

Ya bayyana cewa wasu shuwagabannin tsaro sun halarci tattaunawan a lokaci Abba Marama, wanda kungiyar ta kama, ta kuma sako tare da wasika zuwa ga Jonathan.

KU KARANTA KUMA: Abun al’ajabi: An yiwa yan majalisa masu barin gado gwanjon kayayyakin ofis na miliyan 3 akan N367,479

Jigon har ila yau yayi roko ga kungiyar ta’addan da su daina daukaka myagun ayyukanta a kasar, inda ya kara da cewa kamar yanda aka sani, Najeriya bata da wata kasa banda wanda yan ta’addan ke ciki.

Haka zalika, Legit.ng ta rahoto a baya cewa tsohon shugaban majalisa kuma sakataren kungiyar amintattu na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Sanata Adolphus Wabara, ya bayyana cewa da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya dauki shawaransa na cewa kada ya tsaya takara a zaben 2015, toh da jam’iyyar bata fadi a zaben shugaban kasa ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel