Kotu ta kara kwace kujerar majalisar wakilai daga hannun APC, ta umar INEC ta bawa PDP

Kotu ta kara kwace kujerar majalisar wakilai daga hannun APC, ta umar INEC ta bawa PDP

A ranar Litinin ne wata kotun gwamnatin tarayya dake zamanata a Owerri ta yanke hukuncin karbe kujerar majalisar wakilai ta mazabar Nkwerre/Nwangele/Njaba?Isu daga hannun Ugonna Ozurigbo, dan takarar da aka bawa shaidar ya ci zabe a karkashin inuwar jam'iyyar APC.

A cikin makon da ya gabata ne Ozurigbo ya yi murabus daga mukaminsa na mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Imo.

Da yake yanke hukunci, Alkalin kotun, Jastis P. A. Rigime, ya umarci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da ta janye shaidar cin zaben da ta bawa Ozurigbo tare da mika ta ga Kingsley Echendu, dan takarar jam'iyyar PDP.

Jam'iyyar PDP da dan takarar ta basa cikin wadanda suka shigar da kara kotu a kan zaben Ozurigbo.

Kotu ta kara kwace kujerar majalisar wakilai daga hannun APC, ta umar INEC ta bawa PDP

Rochas Okorocha; gwamnan jihar Imo
Source: Twitter

Kotun ta bayyana cewar Harrison Nwadike, wanda ya shigar da kara, ne halastaccen dan takarar da ya lashe zaben fidda 'yan takara na mazabar da jam'iyyar APC ta gudanar.

Nwadike ya shigar da karar jam'iyyar APC da hukumar zabe a kan gabatar da sunan Ozurigbo ga masu zabe a matsayin dan takara bayan shine wanda ya lashe zaben cikin gida.

Saidai, bayan kotun ta yanke wannan hukunci, Nwadike ya shaida wa manema labarai cewar duk da ya amince da hukuncin kotun a kan cewar shine halastaccen dan takara, kuskure ne kotun ta bayyana dan takarar jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya yi nasara.

Ya kara da cewa zai daukaka kara domin kalubalantar bangaren hukuncin kotun da ya bayyana a mika kujerar ga dan takarar PDP, ya na mai bayyana cewar kamata ya yi kotun ta bashi kujerar tunda dai shine halastaccen dan takarar jamiyyar APC, wacce jama'a suka zaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel