Shugaban kasa Buhari ya gana da sarakunan kudu maso kudu a fadarsa

Shugaban kasa Buhari ya gana da sarakunan kudu maso kudu a fadarsa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a halin yanzu yana ganawar sirri tare da kungiyan sarakunan yankin kudu.

Ganawar ya fara ne misalin karfe 11.37 na safe a majalisar fadar shugaban kasa, Abuja.

Har ila yau dai ba a bayana cikakken bayanin ganawar tasu kamar yanda ake cigaba da ganawan a lokacin da aka tattara wannan rahoton.

Shugaban kasa Buhari ya gana da sarakunan kudu maso kudu a fadarsa

Shugaban kasa Buhari ya gana da sarakunan kudu maso kudu a fadarsa
Source: UGC

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 27, a Abuja ya sa hannu a kasafin kudin 2019.

Majalisar dokoki a baya ta amince da kasafin kudin 2019 mai dauke da kimanin N8.92trn fiye da naira N8.83trn da shugaban kasa Buhari ya sa hannu a ranar 18 ga watan Disamba, 2018.

Karin N90bn a kasafin kudin ya kasance na magance kalubalen da fannin tsaro ke fuskanta a kasar,da kudi ga yan majalisa da taimako ga jihar Zamfara.

KU KARANTA KUMA: Canje-canje da majalisa tayi zasu shafi aiwatar da kasafin kudin 2019 - Buhari

Amman da yake sa hannu a kasafin kudin a ranar Litinin, shugaban kasa Buhari yayi kotafi akan kari da aka samu a kasafin kudin, wanda yazo sanadiyan karin sabbin ayyuka.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel