Rashin Tsaro: Buhari ya gana da gwamnonin Arewa a fadar Villa

Rashin Tsaro: Buhari ya gana da gwamnonin Arewa a fadar Villa

A yayin ci gaba da ta'azaarar kalubale na rashin tsaro a kasar nan, shugaban kasa Muhammadu Buhari a halin yanzu ya shiga bayan labule wajen gudanar da taron gaggawa tare da dukkanin gwamnonin Arewa a fadar sa ta Villa dake garin Abuja.

Rashin Tsaro: Buhari ya gana da gwamnonin Arewa a fadar Villa

Rashin Tsaro: Buhari ya gana da gwamnonin Arewa a fadar Villa
Source: Twitter

Rahotanni kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito sun bayyana cewa, ganawa tsakanin shugaba Buhari da gwamnonin Arewacin Najeriya ta fara gudana ne da misalin karfe 12.30 na ranar Litinin a babban dakin taro na Council Chambers dake fadar shugaban kasa.

Ganawar ta sirrance tsakanin shugaban kasa Buhari da gwamnonin Arewa ta fara gudana bayan ganawar sa da kungiyar sarakunan gargajiya na yankin Kudu maso Kudancin Najeriya.

Gwamnonin dake halartar taron a fadar shugaban kasa sun hadar da Abdulaziz Yari (Zamfara), Kashim Shettima (Borno), Nasir El-Rufa'i (Kaduna), Aminu Bello Masari (Katsina), da kuma Aminu Waziri Tambuwal (Sakkwato).

KARANTA KUMA: Hukumar NDLEA za ta gudanar da bincike akan sabbin manyan sakatarorin gwamnatin Kano - Ganduje

Sauran gwamnonin da a halin yanzu suke tsaka da ganawa da shugaba Buhari sun hadar da; Muhammad Baduru Abubakar (Jigawa), Yahaya Bello (Kogi), Atiku Bagudu(Kebbi), Simon Lalong (Filato), da kuma Abubakar Sani Bello (Neja).

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel