Canje-canje da majalisa tayi zasu shafi aiwatar da kasafin kudin 2019 - Buhari

Canje-canje da majalisa tayi zasu shafi aiwatar da kasafin kudin 2019 - Buhari

Bayan sanya hannu a kasafin kudin 2019, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa wasu sauye-sauyen da majalisar dokokin kasar ta shigar zai shafi gudanarwar kasafin kudin.

Yayin da yake sa hannu a kasafin kudin a fadar shugaban kasa, Abuja, a yau Litinin, 27 ga watan Mayu, shugaba Buhari yace majalisar dokokin kasar ta rage wasu adadin ayyuka a wasu bangarori sannan ta kuma kara a wasu bangarori.

Majalisan dokokin kasar a ranar 30 ga watan Afrilu na wannan shekarar ta amince da kasafin kudin 2019 mai dauke da kimanin naira triliyan 8.916.

Canje-canje da majalisa tayi zasu shafi aiwatar da kasafin kudin 2019 - Buhari

Canje-canje da majalisa tayi zasu shafi aiwatar da kasafin kudin 2019 - Buhari
Source: Twitter

Yawan kudin da majalisan ta sa hannu ya hau da sama da naira biliyan 90 da naira triliyan 8.826 din da shugaban kasa Buhari ya fara gabatarwa a rabar 19 ga watan Disamba na shekaran da ya gabata inda ya gabatar da kasafin kudi ga majalisun biyu.

Buhari yace zai tabbatar shugabancin majalisun masu jiran gado sun magance dumuwar dake tattare cikin kasafin kudin da majalisar ta amince da shi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya sanya hannu a kasafin kudin 2019

An tattaro cewa shugaban majalisan dattawa Bukola Saraki ya isa taron bikin sa hannu a kasafin kudin.

Kakakin majalisan wakilai, Yakubu Dogara, mataimakin shugaban majalisan dattawa, Ike Ekweremadu, da sauran mambobin majalisan duk sun halarci taron.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel